Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin jihar Kano a hukumance ta kaddamar da jigilar alhazai na farko na aikin hajjin 2025 zuwa kasar Saudiyya.
Mataimakin Gwamna Aminu Abdulsalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jaddada aniyar gwamnatin na ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta shirya tsaf domin kare jin dadin alhazanta da suka hada da samar da wurin kwana, ciyarwa, da tallafi na gaba daya a duk lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Ya yi nuni da cewa gwamnatin jihar ta yi tsayuwar daka wajen kiyaye jin dadin alhazanta da suka hada da samar da masauki, ciyarwa, da tallafi na gaba daya.
Mataimakin Gwamnan Kano Kwamared Gwarzo ya bukaci maniyyatan da su kasance masu da’a, hakuri, da mutuntawa, inda ya karfafa musu gwiwar zama jakadu nagari na jihar Kano da Najeriya baki daya.
Wakilinmu na ofishin mataimakin gwamna ya ruwaito cewar taron kaddamar da tuta ya samu halartar Mai Martaba Sarkin Kano na 16, Mai Martaba Muhammadu Sanusi II, da ‘yan majalisar zartarwa ta jiha, da shugabannin kananan hukumomi, da sauran manyan baki.