Daga: Abdullahi Bashir
Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi a gaban shugabannin ƙasashe da gwamnatoci a zama na 81 na Babbar Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA), wanda za a gudanar a hedikwatar Majalisar Ɗinkin Duniya da ke birnin New York na ƙasar Amurka a watan Satumba.
Wakilin Najeriya na dindindin a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Sanata Jimoh Ibrahim, ne ya bayyana hakan bayan ya yi wa Shugaba Tinubu bayani kan shirye-shiryen taron a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

A cewarsa, Shugaba Tinubu zai yi amfani da dandalin taron wajen bayyana irin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ke aiwatarwa, da ci gaban da aka samu a fannonin shugabanci, tare da jawo hankalin masu zuba jari zuwa Najeriya.
Ya ce ana kuma sa ran shugaban ƙasar zai gudanar da jerin ganawa da shugabannin ƙasashe da manyan jami’an ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa domin tattauna batutuwan da suka shafi tsaro, tattalin arziki, sauyin yanayi da bunƙasa haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa.

Taron Babbar Majalisar Ɗinkin Duniya na 81 zai haɗa shugabanni daga ƙasashe mambobin MDD domin tattauna manyan batutuwan da suka shafi zaman lafiya, ci gaba mai ɗorewa, tattalin arziki da sauran ƙalubalen da ke fuskantar duniya.