Daga: Ibrahim Sani Gama

Sabon Kwamishinan Jihar Delta, Moses Ogodo, ya kasa riƙe hawayensa yayin bikin rantsar da shi a matsayin sabon mamba na Majalisar Zartarwar Jihar.

Moses Ogodo ya fashe da kuka ne jim kaɗan bayan kammala rantsar da shi a wani biki da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar Delta da ke Asaba.

A cikin wani yanayi mai cike da tausayi, sabon kwamishinan ya nufi wurin Gwamna Sheriff Oborevwori da alama domin nuna godiya, inda ya yi ƙoƙarin durƙusawa a gabansa.

Sai dai gwamnan ya hana shi, inda ya ce masa: “Kada ka durƙusa mini. Tashi tsaye. Mun zo ne domin yi wa al’ummar Delta hidima tare.”

Lamarin ya jawo tafi da murna daga mahalarta taron, yayin da aka ga sabon kwamishinan yana share hawaye.

Mai taimaka wa gwamnan na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ossai Ovie Success, ya bayyana lamarin a matsayin “hawaye na farin ciki”, yana mai cewa abin ya nuna tawali’u da salon jagorancin Gwamna Oborevwori.

Gwamna Oborevwori ya kuma buƙaci sabbin kwamishinonin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, ƙwarewa, riƙon amana da kishin yi wa jama’a hidima.

An rantsar da Moses Ogodo da Brave Enodeh a matsayin sabbin kwamishinonin jihar, yayin da wasu jami’an gwamnati kuma suka karɓi wasu muƙamai na gwamnati.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kim Jong Un Ya Fara Nuna ’Yarsa Mai Shekara 13 A Matsayin Magajiyarsa

Daga: Abdullahi Bashir Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim…

Fiye da Matasa 6,000 da Masu Horarwa Sun Yi Rijista Don Gasar Matasa ta Kasa a Asaba

Daga: Zaharaddeen Saleh Hukumar wasanni ta Kasa ta tabbatar da cewa jimillar ‘yan…

Cigaba Da Ayyukan Alheri Bayan Ramadan Alama Ce Ta Karɓuwar Ibadar Bawa — Sheikh Kamalu Inuwa

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa Cigaba da aikata kyawawan ayyuka bayan watan Ramadan na…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Samu Lambar Yabo A Matsayin Jihar Da Ke Yaki Da Yin Bahaya A Fili

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, mai…