Daga: Abdullahi Bashir

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, ya fara nuna ’yarsa mai shekara 13, Kim Ju Ae, a matsayin wadda za ta gaje shi a mulki.

Hukumar leƙen asiri ta Koriya ta Kudu, wato National Intelligence Service (NIS), ce ta bayyana hakan yayin da take yi wa ’yan majalisa bayani, inda ta ce ta cimma wannan matsaya ne bayan nazarin wasu alamu da dama.

A cewar rahotanni, Kim Ju Ae ta rika bayyana tare da mahaifinta a wurare daban-daban na gwamnati, ciki har da bikin soji da gwaje-gwajen makamai, lamarin da masana ke ganin yana iya nuna kokarin daga darajarta a idon jama’a.

Sai dai har yanzu gwamnatin Koriya ta Arewa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da batun wanda zai gaji Kim Jong Un ba, yayin da harkokin mulki a kasar ke kasancewa cikin tsananin sirri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Nuna Alhini Kan Rasuwar ‘Yan Wasan Kano 21 A Gasar Wasanni Ta Kasa

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Jami’ar Bayero Kano kuma Shugaban…

Gwamna Abba Ya Karɓi Baƙuncin Tawagar Gwamnatin Jihar Borno

Daga: Sani Idris Maiwaya Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir…

Matsayar Saudiyya Kan Ranar Ƙaramar Sallah

Daga: Idris Aliyu Ishaq Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa ba…

Kano Ta Shirya Hada Kai Da Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu Don Kara Inganta Ilimi a Jihar

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin Jihar Kano ta jaddada kudirinta na bai…