Daga: Shehu Suleiman Sharfadi

Gwamnatin jihar Kano ta gargadi iyaye maza da mata da su kaucewa dabi’ar nan ta yiwa ‘ya’yansu auren dole wanda yinsa ke haifar da mummunan sakamako a tsakanin maaurata.
Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ne yayi wannan gargadin yayin taron liyafar daurin auren ‘ya’yan mataimakin gwamnan Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo wanda ya gudana a birnin Kano.
A yayin daurin auren a masallacin juma’a na Alfur’qan, Gwamna Yusuf ne yayi wa Amina Aminu Abdussalam Gwarzo uban Amarya yayin da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yayi wa Nusaiba Aminu Abdussalam Gwarzo uban Amarya bisa sadaki naira dubu dari biyu biyu.
Gwamnan ya sanya albarka tare kuma da yiwa ma’auratan fatan alkhairi da yi musu addu’ar dorewar zaman lafiya da kara dankon soyayya a tsakanin ma’auratan.
Gwamnan ya bayyana cewar, iyaye da ma’aurata suna da hakki akan aure ta yadda duk wanda ya taimaka aka tursasa yin auren dole kuma wani abu ya biyo baya to su tabbatar suna da kamasho.
Don haka, ya yi kira ga sarakuna da malamai cewa ya zama wajibi su tashi tsaye wajen fadakar da iyaye illar tursasa yaya auren da basa so.
Shima anasa bangaren, dan majalisar tarayya mai wakiltar Gezawa da Gabasawa Muhammad Chiroma yayi fatan alkhairi tare kuma da addu’ar dorewar zaman lafiya Allah ya cigaba da riko da hannayensu wajen sauke nauyin da aka dora musu.

Shima anasa bangaren daya daga cikin mahalarta daurin auren, Bello Yayo Dahiru Gwarzo ya shawarci amaren su yiwa mazajensu biyayya sannan suma mazajensu su kula da hakkokin iyalan su.
Daganan kuma, sai yayi musu fatan alkhairi tare kuma da dorewar zaman lafiya da kuma kaunar juna.
Wakilinmu ya ruwaito cewar, taron ya samu halartar wakilan mataimakin gwamnan jihohin Katsina, Yobe da manyan sakatarorin gwamnatin jihar da kwamishinoni da sauran mukarraban gwamnati.