Daga: Abdullahi Bashir
Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta soke hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke, wanda ya bai wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) umarnin cire rajistar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Accord Party da wasu jam’iyyun siyasa uku.
A hukuncin da ta yanke ranar Talata, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta bayyana cewa hukuncin Babbar Kotun Tarayyar da ya umarci INEC ta cire rajistar jam’iyyun siyasar “ba shi da inganci kuma ba shi da wani tasiri a doka.”

Kwamitin alkalai uku na Kotun Ɗaukaka Ƙarar, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Justice Abba Mohammed, ya yanke wannan hukunci baki ɗaya ba tare da wani sabani ba.
Kotun ta bayyana cewa Babbar Kotun Tarayya ba ta da hurumin shari’a (jurisdiction) na sauraron ƙarar tun daga farko, saboda haka duk hukuncin da ta yanke kan lamarin ya zama maras inganci.

Da wannan hukunci, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta soke umarnin da ya bai wa INEC damar cire rajistar jam’iyyun da abin ya shafa, lamarin da ya tabbatar da cewa ADC, Accord Party da sauran jam’iyyun da ke cikin ƙarar ba su rasa rajistarsu bisa wannan hukunci ba.
Ana sa ran wannan hukunci zai yi tasiri ga tsarin jam’iyyun siyasa da kuma batutuwan da suka shafi ikon kotuna wajen duba matakan da hukumar zaɓe ke ɗauka kan rajistar jam’iyyu a Najeriya.