Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da suka dawo daga gasar wasannin motsa jiki na kasa da aka kammala kwanan nan a garin Abeokuta na jihar Ogun, gwamnatin jihar Kano ta ci gaba da karbar ta’aziyya.
A yau ne mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya karbi bakuncin ayarin jamiar Al-hikma dake garin ilori a jihar kwara karkashin jagorancin shugaban jami’ar farfesa Nuhu Yusuf wadanda suka kawo ziyarar taaziyya ga gwamnatin jihar Kano.
Farfesa Nuhu ya kuma bayyana cewar sun zo kano ne domin mika sakon taaziyyar wanda ya kafa jamiar Abdurrahim Oladimeji wanda ya yi musu adduar samun rahamar ubangiji.
Sannan kuma shugaban jami’ar farfesa Nuhu Yusuf ya kara da cewar jamiar zata baiwa iyalan mamatan gurbin karatun mutum uku kyauta a jami’ar.
Shima anasa jawabin kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya gode musu bisa wannan gudunmowar karatu da zasu baiwa iyalan mamatan tare kuma da basu tabbacin hadin kai da goyon baya musamman alakar karatu.

Kazalika, ayarin hukumar kashe gobara karkashin jagorancin Daraktan Hukumar dake kano Alhaji sani Abbas wanda suma mataimakin gwamnan ya tarbesu.
Alhaji sani Abbas ya mika ta’aziyyar su ga gwamnatin jihar kano da ma al’ummar ta tare kuma da yi musu addu’ar samun rahamar ubangiji.
Wakilinmu na ofishin mataimakin gwamnan jihar nan Shehu Suleiman Sharfadi ya ruwaito cewar kungiyoyi da jami’an gwamnati daga bangarori daban daban na kawo ziyarar ta’aziyya jihar Kano.
