Daga: Abdullahi Bashir

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da ware Naira biliyan 46 domin sake gina titin sauka da tashin jiragen sama na Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama da Raya Sararin Samaniya ya bayyana cewa, aikin na daga cikin shirye-shiryen gwamnatin tarayya na inganta tsaro da samar da ingantattun kayayyakin more rayuwa a manyan filayen jiragen saman ƙasar.

A cewarsa, titin jiragen saman na Kano ya dade yana buƙatar cikakken gyara saboda yawan amfani da shi da kuma muhimmancin filin jirgin saman ga zirga-zirgar fasinjoji da harkokin kasuwanci a Arewacin Najeriya.

Ana sa ran fara aikin nan ba da jimawa ba, yayin da gwamnati ta ce zai taimaka wajen inganta harkokin sufurin jiragen sama da bunƙasa tattalin arzikin jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kungiyar Agajin Musulmi Za Ta Haɗa Gwiwa da Ma’aikatar Jinƙai Don Tallafa wa Mabuƙata

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Kwamishinan Ma’aikatar Jin Кai da Rage Talauci ta jihar…

NLC Ta Gargadi Gwamnati Kan Tsadar Rayuwa Da Rashin Tsaro

Daga: Abdullahi Bashir Kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ta bayyana damuwa kan yadda…

Rundunar Yaki da Satar Waya a Kano Ta Kama Matashi Kan Zargin Satar Wayoyi da Sayar da Kayayyakin Mata

Daga: Sani Idris Maiwaya Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force (KOSSAP) a…

Kungiyar sakwatawa mazauna jihar Kano ta jaddada kudirinta na tallafawa ‘ya’yan ta domin ganin sun dogara da Kawunansu.

Kungiyar sakwatawa mazauna jihar Kano ta jaddada kudirinta na tallafawa ‘ya’yan ta…