Daga: Mukhtar Yahaya Shehu 

Kwamishinan Ma’aikatar Jin Кai da Rage Talauci ta jihar Kano Aliyu Adamu Kibiya, ya bayyana aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yin haɗin gwiwa da ƙungiyoyin bayar da tallafi domin inganta rayuwar marasa galihu.

Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar wata tawaga daga Muslim Charity Organisation wadda ta kai masa ziyara a ofishinsa.

Idan Za a iya tunawa cewa ƙungiyar, wadda ke da shelkwata a ƙasar Ingila, a kwanan nan ta bayar da gudummawar mota bas mai kujeru 32 ga ma’aikatar domin sauƙaƙa gudanar da ayyukan jin ƙai. Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya karɓi gudummawar a madadin ma’aikatar.

Cikin sanarwa Mai dauke da sa hannun Daraktan sashin wayar da Kan Al’uma na ma’aikatar Ibrahim Abdullahi Kibiya ya bayyana cewa daga cikin manyan ayyukan da aka ɗora wa ma’aikatar akwai samar da ayyukan jin ƙai ga al’ummar jihar, musamman marasa galihu, domin tallafa musu a fannoni daban-daban na rayuwa.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar na maraba da ƙungiyoyin jin ƙai da ke son taimaka wa gwamnati wajen tallafa wa jama’a ta hanyar koyar da sana’o’i, bayar da horon sana’o’i da sauran shirye-shiryen tallafi, yana mai gode wa ƙungiyar bisa gudummawar motar da ta bayar, ya ce hakan zai taimaka matuƙa wajen aiwatar da ayyukan jin ƙai a faɗin jihar.

Kwamishinan ya nemi ƙungiyar ta taimaka wa ma’aikatar wajen aiwatar da wasu ayyuka da suka haɗa da bayar da tallafi, tattara bayanai ta hanyar fasahar zamani, tallafa wa almajirai da samar da kayan makaranta da jakunkuna ga yara ɗalibai, ya ce kowane daga cikin waɗannan ayyuka yana da manufar inganta rayuwar al’umma da jin daɗin mabuƙata.

Tun da farko, Daraktan Shirye-shirye na ƙungiyar, Irfan Rajput, ya ce sun kai ziyarar ne domin ƙarfafa alaƙar da ke tsakaninsu da ma’aikatar tare da tsara hanyoyin ci gaba da aiki tare domin inganta rayuwar marasa galihu.

Rajput ya ce za su kalli waɗannan buƙatu da ma’aikatar ta nema don ganin hanyar da za su shigo su taimaka, har ma da kawo ayyukan jin ƙai masu yawa jihar Kano.

Ya tabbatar da cewa ƙungiyar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da ma’aikatar domin tabbatar da nasarar aiwatar da waɗannan ayyuka a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Matsayar Saudiyya Kan Ranar Ƙaramar Sallah

Daga: Idris Aliyu Ishaq Mahukunta a ƙasar Saudiyya sun sanar da cewa ba…

Shekarau Gains Tinubu Support Groups’ Backing After Gov. Abba’s Endorsement

By: Mukhtar Yahaya Shehu  The Tinubu Support Groups under the leadership of Dr.…

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirin Hada Gwiwa da Kungiyar Injiniyoyi ta Kasa Don Tabbatar da Ingancin Ayyuka

Daga: Ibrahim Sani Gama Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci…

ANPP Na Bukatar Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa: Shin APC Zata Fuskanci Barazana ne?

Daga: Yakubu Abubakar Gwagwarwa Masana harkokin siyasa na bayyana cewa jam’iyyar APC…