Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa
A kokarinta na kara bunkasa harkokin ilimi, gidauniyar cigaban al’umma mai suna SABATURE FOUNDATION ta bada tallafin naira Dubu Dari Biyar (#500,000) ga dalibai marayu da daliban da suka yi fice a sakamakon jarabawarsu ta karshen zangon karatu da kuma malaman makaranta na Alkausara Secondary, Nursery and Primary School ASNAPS Dawakin Tofa Kano, Nigeria.
Shugaban gidauniyar, Mai Magana da Yuwun Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif kuma Babban Daraktan Yada Labaran Gidan Gwamnatin Jihar Kano DG Sanusi Ahmad Bature Dawakin Tofa ya baiyana bayar da tallafin #500 ne din ce a yayin taron gabatar da Jawabai da Raba kyautuka (Speech and Prize Giving Day Ceremony) da makarantar ASNAPS ta gudanar a ranar Lahadi 27/07/2025.

Jim kadan da karrama DG Sanusi Bature a sakamakon taimakawa harkokin ilimin a fadin karamar hukumarsa ta haihuwa, sai DG ya yabawa Alhaji Kabiru Ali kasancewarsa mutum na farko a tarihi da ya fara assasa makaranta mai zaman kanta a yankin karamar hukumar Dawakin Tofa.
“Ya kara da cewa a sakamakon taimakawa dalibai marayu da jagoran makarantar ASNAPS ke yi na karbar ragin kaso hamsin cikin dari na kudin makarantarsu, DG ya bada tallafin #300,000 don a cigaban da biya musu ragowa kason zuwa wani lokaci, ya sake bada #100,000 ga daliban da suka yi fice a jarabawarsu ta karshen zango karatu na wannan shekara, sai #100,000 ga malamansu a bisa kokarin da suke na koyor da daliban”.
Alhaji Kabiru Ali, ya godewa duk wadanda suke tallafawa makarantar ta kowacce fuska, wanda hakan ya sa makarantar ke kara cigaba da daukaka, dalili ta fara ne da bude sashen Islamiyya, Nursery da Primary, ta cigaba zuwa matakin Junior Secondary, yanzu har ta kai tana da sashen babbar sakandire. A don haka ya ke kira ga iyaye da su rika kawo yaransu makarantarsa don samun tarbiyya da karatu mai inganci.

A yayin taron an karrama wasu karin muhimman mutane uku da suke tallafawa harkokin ilimin a matakin karamar hukuma su ne shugaban karamar hukumar Dawakin Tofa Anas Muktar Bello Danmaliki, Alh. Ahmad Tijjani Abdullahi da Prof. Kabiru Bello Dungurawa sai wasu iyayen daliban su 15, da dalibai uku-uku daga kowanne aji na ‘Primary zuwa Secondary’ wadanda suka yi fice a sakamakon jarabawarsu a makarantar ASNAPS wadda aka assasata tun a shekara ta 1996.
