Daga: Ibrahim Sani Gama 

 

Kungiyar kwankwasiyya singa market dake nan jihar kano, ta yabawa Gwamnan kano injiniya Ababa Kabir yusuf bisa yadda ya nuna goyan bayansa ga kungiyar a lokacin daya dawo daga kasa mai tsarki a matsayinsa na Amirul hajji da kuma gudanar da aikin hajjin ban a.

 

 

.Shugaban kungiyar Alh. Muntari Liti Kwasamgwami ne ya yi wannan yabon jim kadan bayan wucewar Gwamnan ta kasuwar singa domin nuna godiyarsa ga yankwankwasiyya na kasuwar singa da sauran Alummar jihar kano da suke gudanar da kasuwanci a ciki da wajen kasuwar ta kwanar singa..

 

 

Alh. Liti kwasamkwami ya bayyana cewar, yankungiyar kwankwasyya Singa market sun dade suna baiwa kwankwasiyya cikakkiyar gudunmawa ta fannoni da dama domin ganin Abba Kabir ta lashe zaben daya gabata,wanda kuma cikin ikon Allah aka samu nasara tun daga lokutan zabe har da yayin zuwa kotu,wanda daga bisani aka tabbatar Alhaji Abba Kabir a matsayin wanda ya ci zaben.

 

.

Shugaban kungiyar ya bayyana cewar,baya ga haka kungiyar sai da tayi saukar karatun alkur’ani maigirma sau dubu daya domin ganin Gwamnatin jihar kano ta samu gagarumar nasara akan duk wani abu da ta sanya a gaba na hidimtawa alummar jihar kano wanda yanzu duk titin da ka bi za ka ga Gwamnatin jinar kano karkashin jagorancin injiniya Abba Kabir yusuf tana gudanar da ayyuka da fitar da magudanan ruwa domin kaucewa ambaliyar ruwa wannan ba karamar nasara bace ga alummar jihar .

 

 

.Shugaban yace ta fannin ilimi tun daga matakin furaimari zuwa sakandire da manya makarantu da jami’o’in na jihar kano an samu babbar nasara da za’a dade ana cin gajiyar irin wadannan ayyuka .

,haka zalika, a bangaren tsaro da samar da zaman lafiya domin kare rayuka da dukiyoyin alummar jihar kano ba,a bar shi a baya ba.

.Alh. Muntari Liti Kwasamgwami yayi kira ga Gwamnatin jihar kano karkashin jagorancin Abba Kabir yusuf, daya tuna da kungiyar kwankwasiyya singa market a rika sanya ta a cikin duk wasu abubuwa da suka taso a cikin ayyukan gwamnati domin ba da gudunmawa, musamman abin da ya shafi harkokin kasuwanci da abin daya taba yankasuwa,inda yace,yanzu haka ‘yan hamayya da suke kusa da su a cikin kasuwa dariya suke musu wanda suke ganin kamar sun tura motane ta bulesu da hayaki,.Shugaban kungiyar yace ya kamata maigirma Gwamnan kano Abba Kabir yusuf taimakawa wannan kungiya domin karfinta yana neman karewa saboda rashin tallafin daga gwamnatin wanda komai da karfi da jikinta take yi domin ganin gwamnatin kano ba ta durkushe ba akan aikace-aikacenta na yau da kullum.

Shugaban ya godewa gwamnan bisa yadda ya rika tiri-tiri da mahajjatan jihar kano musamman wadanda suka hadu da iftilin gobara a lokacin aikin hajji da yadda ya rabawa mahajjatan jihar kano riyal dari uku-uku domin tallafa musu.

Daga karshe ya bayyana cewar, kungiyar kwankwasiyya singa market ba za ta gajiya ba wajen bayyana ayyukan gwamnati a ciki da wajen kasuwar singa kamar yadda ta saba,inda kuma,ya bukaci alummar kasuwar singa da su ci gaba da baiwa Gwamnatin jihar kano goyan bayan da suka kamata domin ganin ta samu damar aiwatar da ayyukan ci gaba ga alummar jihar kano baki daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Watsi Da Abincin Da Ake Bai Wa Alhazan Najeriya A Hajji

Daga: Abdullahi Bashir Hukumar Alhazai ta Kasa, National Hajj Commission of Nigeria…

Kwamishinan Agaji Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar ’Yan Majalisar Dokokin Kano Biyu

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci na Jihar…

Ali Dalori: Ya Karɓi Ragamar APC Na Ƙasa, Ya Yi Alkawarin Ƙarfafa Haɗin Kai Da Jagoranci Na Gaskiya

Daga: Hamza Garba Yakasai Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC na ƙasa,…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Jajantawa Iyalan Sheik Dan Almajiri Bisa Rasuwarsa

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo,…