Daga: Shehu Suleiman Sharfadi 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Sayyadi Barhama Dan Almajiri, Mataimakin Babban Limamin Masallacin Juma’a na Taibah da ke Rijiyar Lemo, wanda ya rasu a ranar Talata bayan gajeriyar rashin lafiya yana da shekaru 70 a duniya.

Marigayin malamin addinin ya kasance babban yayan Barrista Bashir Dan Almajiri. Ya rasu ya bar mata guda daya, ’ya’ya takwas da jikoki.

Yayin ziyarar, Garo ya bayyana rasuwar fitaccen malamin addinin da cewa, “hakika wannan babban rashi ne ba ga iyalansa kadai ba, har ma da al’ummar Musulmi da daukacin Jihar Kano baki daya.”

Mataimakin Gwamnan ya kuma baiwa iyalansa da yan uwa hakurin jure rashin tare kuma da yi masa adduar fatan samun rahamar subhanahu wa ta’ala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Ali Dalori: Ya Karɓi Ragamar APC Na Ƙasa, Ya Yi Alkawarin Ƙarfafa Haɗin Kai Da Jagoranci Na Gaskiya

Daga: Hamza Garba Yakasai Shugaban rikon kwarya na jam’iyyar APC na ƙasa,…

Dandazon al’umma sun tarbi gwamnan Kano biyo bayan dawowarsa daga kasa Mai tsarki

Daga: Adamu Dabo   A yau laraba dubban al’ummar jihar Kano daga…

Zamu Ci Gaba Da Baiwa Gwamnatin Jihar Kano Hadin Kai Domin Samar Da Tsaro Da Dakile Masu Kwacen Wayoyin Al’umma.

Daga: Ibrahim Sani Gama   Kungiyar ‘Yan Kasuwar Rimi da ke Jihar Kano…

KANO: Shugaban Kungiyar Inna Mafita Ya Gargadi Masu Iƙirarin Mallaka

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa Shugaban Kungiyar Inna Mafita a Jihar Kano, Alhaji Abdullahi…