Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Murtala Sule Garo, ya jagoranci zaman sulhu tsakanin masu neman takarar kujerar Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Rogo da Karaye, domin tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin ’yan jam’iyyar APC.
Wata sanarwa da daya daga cikin masu taimakawa Mataimakin Gwamnan kan harkokin yada labarai, Salmanu Rabi’u Gwarzo, ya fitar ta bayyana cewa zaman sulhun ya kai ga cimma matsaya tsakanin ’yan takarar, inda Alhaji Ibrahim Ahmad Karaye ya amince da janyewa Alhaji Abdullahi Sani Rogo takara cikin mutuntawa da fahimtar juna.

Taron ya gudana ne a gaban Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar daga kananan hukumomin Karaye da Rogo.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman sulhun akwai Alhaji Balarabe Isyaku Karaye, tsohon Shugaban Karamar Hukumar Karaye, Alhaji Naseer Abdullahi Dutsen Amare, tsohon Dan Majalisar Jiha mai wakiltar Karaye, da kuma Alhaji Idi Zare Rogo.

An gudanar da zaman sulhun ne a yammacin ranar Alhamis a ofishin Mataimakin Gwamna da ke gidan gwamnati.
Mahalarta taron sun jaddada bukatar ci gaba da zaman lafiya, hadin kai da kuma karfafa dankon zumunci a tsakanin ’ya’yan jam’iyyar APC.