Daga: Muhammad Adamu Abubakar
Hukumar kula da kayayyakin amfanin gona da ake shigowa da fitar da su ta ƙasa ta shawarci al’umma da su riƙa tabbatar da ingancin kayayyakin da suke saya ko safararsu.

Jami’i a hukumar mai kula da shiyyar Arewa maso Yamma, ACG Dr. Gano Adamu Isah, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano.
Ya ce, hukumarsu na aiki a kan iyakokin tudu da kuma na ruwa domin tabbatar da bin ƙa’idoji da kuma hana shigo da kayayyakin da ba su da inganci.

ACG Dr. Gano Adamu Isah ya ƙara da cewa ma’aikatan hukumar na aiki tsawon sa’o’i 24 a kowace rana domin kula da kayayyakin amfanin gona da ake shigowa da fitar da su, tare da duba ingancinsu.
Haka kuma ya bayyana cewa daga cikin ayyukan da suke yi har da tantance sahihancin kayayyakin amfanin gona da ake safararsu.
Ya ƙara da cewa hukumar na aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin da suke da alaƙar aiki da su domin tabbatar da inganci da tsaron kayayyaki.