Daga: Ibrahim Sani Gama
Kungiyar masu sana’ar magungunan gargajiya ta jihar Kano, reshen bakin Asibitin Murtala, ta bayyana aniyarta ta ci gaba da bai wa Gwamnatin jihar Kano cikakken hadin kai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a fadin jihar.
Shugaban kungiyar, Alhaji Saidu Salisu, ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar bakin Asibitin Murtala, inda ya ce kungiyar tana taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro a kasuwar da kewaye.

Alhaji Saidu ya ce kungiyar ta kafa kwamiti na musamman domin samar da tsaro a cikin kasuwar da unguwannin Kofar Mata da bakin Asibitin Murtala, inda suke gudanar da harkokinsu na kasuwanci. Ya ce wannan mataki yana daga cikin kokarin kungiyar na tallafawa manufofin gwamnati wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Shugaban ya yi kira ga Gwamnatin Kano da ta sanya kungiyar cikin jerin masu samun tallafi da hadin kai, duba da rawar da take takawa wajen ci gaban jihar, musamman a bangaren tsaro da tattalin arziki.
“Hakika akwai kananan ’yan kasuwa da ke bukatar taimakon gwamnati ta fuskar jari domin kara bunkasa harkokinsu. Idan aka tallafa musu, hakan zai taimaka wajen rage talauci da samar da zaman lafiya mai dorewa,” in ji Alhaji Sa’idu.

Ya kuma shawarci ’yan kasuwa su yi amfani da duk wata dama da gwamnati ta samar wajen inganta sana’o’insu, domin hakan ne zai ba su damar dogaro da kai da kuma kara habaka tattalin arzikin jihar.
Alhaji Saidu ya kara tabbatar da cewa kungiyar masu magungunan gargajiya ta jihar Kano a shirye take ta ci gaba da mara wa Gwamnatin Kano baya domin ganin jihar ta ci gaba a fannonin da dama.
A karshe, ya jinjinawa Gwamnatin Kano bisa kokarinta na raya kasa, musamman a bangaren kasuwanci, gyaran hanyoyi, ci gaban ilimi, da bayar da tallafin jari ga kananan ’yan kasuwa.
Haka kuma, ya yaba wa kwamiti na tsaro na kasuwar bakin Asibitin Murtala bisa yadda yake taka muhimmiyar rawa wajen dakile matsalolin rashin tsaro a kasuwar da makwabtanta.