Daga: Shehu Suleiman Sharfadi 

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya bi sahun manyan baki da sarakunan gargajiya domin murnar zagayowar ranar cika shekaru 25 da kafuwar mai martaba sarkin fune Dakta Saleh Idris ibn usman a kan karagar mulki.

Taron mai cike da tarihi wanda ya gudana a garin Fune dake Damagum a jihar Yobe, ya samu halartar manyan shugabanni, masu rike da sarautar gargajiya, da masu hannu da shuni don karrama wannan gagarumin hidima na sarki.

A yayin bikin, Mai Girma Mataimakin Gwamnan ya kuma halarci daurin auren Fatiha na ‘ya’yan Wazirin Fune, Mai Girma Mataimakin Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Idi Barde.

A wajen nuna zumunci da hadin kai, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya kasance Waliyyi (Mai kula) ga angon Kabir Idi Barde, inda ya gabatar da addu’o’i da fatan alheri da kwanciyar hankali.

Da yake jawabi bayan taron, mataimakin gwamnan ya taya mai martaba sarkin Fune murnar cika shekaru 25 a kan karagar mulki, inda ya yaba da jajircewarsa na samar da hadin kai, kiyaye kayayyakin tarihi, da inganta al’adu.

Ya kuma mika sakon taya murna ga sabbin ma’auratan, inda ya yi addu’ar Allah ya sa zaman nasu ya kasance cikin soyayya, fahimta, da wadata.

Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo ya jaddada kudirin gwamnatin jihar Kano na karfafa alaka da cibiyoyin gargajiya da hada kai a fadin jihohin kasar domin samun zaman lafiya, kwanciyar hankali a fadin kasarnan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Wani Abu Da Al’umma Ya Kamata Su Sani Game Da Turawan Yamma -Dr. Nastura

Daga: Kabir Muhammad Getso Shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa Dr. Nastura Ashir Sharif ya…

Gwamna Abba Ya Sake Zabar Garo a Matsayin Abokin Takararsa na Zaben 2027

Daga: Mas’ud Mayo Garo Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya…

Shugabannin Majalisa Sun Nuna Fargaba Kan Tsananin Ciwo Bashi da Rashin Sa Ido

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, tare da Shugaban…

Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Kammala Tsare-Tsaren Gina Kwalejin Fasaha a Gaya

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi cikakken rahoton ƙarshe…