Daga: Mas’ud Mayo Garo
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da cewa Mataimakinsa, Alhaji Murtala Sule Garo, ne zai ci gaba da kasancewa abokin takararsa a zaben gwamnan jihar da za a gudanar a shekarar 2027.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakin Gwamnan Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Litinin.

A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne yayin wani taron tuntubar masu rike da mukaman gwamnatin tarayya daga Jihar Kano, wadanda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada, wanda aka gudanar a Masaukin Gwamnan Kano da ke Abuja.
Gwamnan ya ce ya yanke wannan hukunci ne sakamakon irin biyayya, jajircewa da kuma gudunmawar da Garo ke bayarwa wajen tafiyar da gwamnati da bunkasa ci gaban Jihar Kano tun bayan hawansa kan mukamin Mataimakin Gwamna.
Ya kara da cewa yana gamsuwa da irin hadin gwiwar da ke tsakaninsu, yana mai bayyana cewa Garo ya nuna kwarewa, himma da cikakken sanin ya kamata wajen gudanar da nauyin da aka dora masa.
A cewarsa, “Ban taba nadamar zaben Garo a matsayin Mataimakina ba. Ya tabbatar da cewa shi ne zabin da ya dace, kuma ina da cikakkiyar kwarin gwiwa a kansa.”
Har ila yau, Gwamna Yusuf ya sake jaddada amincewarsa da Mataimakin Gwamnan, yana mai bayyana shi a matsayin amintaccen abokin aiki wanda gudunmawarsa ke kara karfafa kokarin gwamnatin wajen samar da ci gaba mai dorewa ga al’ummar Jihar Kano.

Sannan ya yi kira ga shugabannin jam’iyya, masu rike da mukaman siyasa da magoya baya da su ci gaba da kasancewa cikin hadin kai tare da mara wa gwamnati baya domin ci gaba da aiwatar da manufofinta gabanin babban zaben shekarar 2027.
Sanarwar ta samu sa hannun Darakta Janar na Yada Labarai da Hulda da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa.