Daga: Abdullahi Bashir
Jam’iyyar APC ta sanar da sakamakon zaɓen fidda gwani na kujerun Majalisar Wakilai ta Tarayya a faɗin Jihar Kaduna, a gaban jami’an Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC).
Sakamakon ya nuna cewa Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya, Tajudeen Abbas ya samu ƙuri’u 930 domin lashe tikitin APC a mazaɓar Zariya.

A mazaɓar Zango Kataf/Jaba kuwa, Amos Gwamna ya samu ƙuri’u 1930, yayin da Arch Hamza Ibrahim ya samu ƙuri’u 1030 a mazaɓar Soba.
A Kaduna ta Arewa, Hon. Samaila Abdulsuleiman ya lashe zaɓen da ƙuri’u 3049, inda Abdulazeez Abubakar Kaka ya samu ƙuri’u 65, sannan Abubakar Mahmud ya samu ƙuri’u 96.

Mukthar Shehu Ladan ya zama ɗan takarar APC a mazaɓar Makarfi/Kudan ta hanyar maslaha, yayin da Ahmad Muhammad Munir ya samu ƙuri’u 1120 a mazaɓar Lere.
A Kaura, Prof Benjamin Gugong ya samu ƙuri’u 1085 inda Hon. Mathew Donatus ya samu ƙuri’u 255, yayin da Mukthar Zakari Chawai ya samu ƙuri’u 1750 a mazaɓar Kauru.
Haka kuma, Fidelix Joseph Bagudu ya samu ƙuri’u 1580 a Chikun/Kajuru, Daniel Amos ya samu ƙuri’u 2110 a Jama’a/Sanga, sannan Gabriel Saleh ya samu ƙuri’u 2590 a Kachia/Kagarko.
Sauran waɗanda suka yi nasara sun haɗa da Abubakar Shehu Giwa mai ƙuri’u 2669 a Birnin Gwari/Giwa, Hussaini Muhammad Jalo mai ƙuri’u 1171 a Igabi, Hussaini Abdulkarim Ahmed mai ƙuri’u 1130 a Kaduna ta Kudu, da Hon. Sadiq Ango Abdullahi mai ƙuri’u 920 a Sabon Gari.
A mazaɓar Ikara/Kubau kuwa, Bashir Suleiman Zuntu ne ya yi nasara da ƙuri’u 1787.