Daga: Mukhtar Yahaya Shehu
Kwamishinan Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci na Jihar Kano, Alhaji Adamu Aliyu Kibiya, ya bayyana matuƙar alhini da jimami kan rasuwar ’yan Majalisar Dokokin Jihar Kano guda biyu, Aminu Sa’ad Ungogo da Sarki Aliyu Daneji, masu wakiltar ƙananan hukumomin Ungogo da Kano Municipal.
A cikin wata sanarwa, Kwamishinan ya ce rasuwar ’yan majalisar babban rashi ne ba ga iyalansu da mazaɓunsu kaɗai ba, har ma ga Jihar Kano da ƙasa baki ɗaya, la’akari da irin rawar da suka taka wajen wakiltar al’ummarsu da gaskiya da jajircewa.
Ya bayyana marigayan a matsayin wakilai nagari da suka sadaukar da kansu wajen hidimar jama’a, inda suka gudanar da ayyukansu cikin tawali’u, riƙon amana da cikakken nauyin alhaki.
Kwamishinan ya ce, “Ni, a madadin iyalina da dukkan ma’aikatan ma’aikatar, ina miƙa ta’aziyyata ga jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata (Dr.) Rabi’u Musa Kwankwaso, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, shugabannin jam’iyyar NNPPP, da kuma iyalan mamatan bisa wannan babban rashi.”
Sanarwar wadda Daraktan Wayar da Kai na Ma’aikatar Harkokin Jin-ƙai da Rage Talauci, Ibrahim Abdullahi, ya sanya wa hannu, ta ce Kwamishinan ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki (SWT) da Ya gafarta wa marigayan kura-kuransu, Ya ba su Aljannatul Firdausi, sannan Ya bai wa iyalansu, mazaɓunsu da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya haƙurin jure wannan babban rashi.