Daga: Ibrahim Sani Gama

Janar Gambo Ahmed Mai Addau mai ritaya ya kasance Shugaban kwamitin hana kwacen waya da yaki da miyagun kwayoyi da fadace-fadacen daba da gwamnati Kano ta kafa a watanni 21 da suka wuce, inda ya bayyana cewa, yanzu haka wannan kwamiti ya gano cibiyoyi har 52 da ake aikata laifuka a Jihar Kano.

Ya kara da cewa, yanzu haka bisa umarni da sahalewar gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir, kwamitin ya dauki matasa 1,050 aiki, wanda kwamishinan harkokin tsaron cikin gida na Kano, Ibrahim Umar ya kaddamar a madadin gwamnan, domin hada hannu da jami’an ‘Yan sanda, NDLEA da Cibil Defence, hukumar leken asiri na farin kaya (DSS), da ‘yan bijilanti da sauransu, domin murkushe munanan ayyukan kwacen waya, fadan daba da harkar miyagun kwayoyi a Kano.

Janar Mai Addau ya tabbatarwa da manema labarai cewa, yanzu haka gwamnatin Kano ta samar da motoci da ababan hawa don kimanin 100 domin yin wannan aikin gadan-gadan da kuma alwashin bayar da duk abun da wadannan zaratan matasa ke bukata don gudanar da wannan aiki na tsare lafiyar al’ummar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Da Dumi-Dumi: Kungiyar Dillalan Rimin Zakara Sun Kori Annitaja Daga Shugabancinta

Daga: Rayyan Hassan Kungiyar dillalan dake Rimin Zakara a karamar hukumar Ungogo,…

Gwamnatin Kano Ta Taya Daukacin Al’ummar Jihar Murnar Barka Da Sallah

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, tare…

Tallafawa Maraya Sila Ce Ta Samun Makwabtaka Da Manzon Allah S.A.W A Aljannah

Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa Malam Ali Yakubu Danjumma ne ya baiyana haka…

Gwamnatin Mu Na Alfahari Da Gidauniyar Dangote

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi    Mataimakin gwamnan jihar Kano kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo…