Daga: Shehu Suleiman sharfadi

Hukumar kula da wasanni ta kasa ta shirya wasan sada zumunta na tsoffin yan wasan kwallon kafa na shiyyar Arewa maso yammacin kasarnan .

Shugaban hukumar kula da wasanni ta kasa malam shehu Dikko ne ya furta hakan yayin da ya jagoranci ayarin hukumar suka kawo wa gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf
Ziyarar ban girma wanda mataimakin gwamnan jihar Alhaji murtala sule Garo a madadin gwamnan ya tarbe su.

Mataimakin gwamnan ya bayyana farin cikinsa bisa wannan ziyarar da kuma gode musu bisa shirya wannan wasan kwallon kafa na sada zumunta.

Ya kuma basu tabbacin gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa basu hadin kai da goyon baya inda ya gode musu bisa zabar jihar kano domin gudanar da wannan wasan kwallon kafa na sada zumunta.

Anasa jawabin shugaban hukumar malam shehu Dikko ya bayyana cewar sun kawo ziyarar ne domin samun tubarraki sannan kuma su taya mai girma mataimakin gwamnan jihar kano Alhaji murtala sule Garo murnar zama mataimakin gwamnan jihar.

Ya kuma bayyana cewar wasan sada zumunta mai taken Northwest veterans All stars renewed hope novelty football match 2026 zai gudana ne a jihar kano.

Dikko ya bayyana cewar sun zo kano ne domin gudanar da wasan kwallon kafa na sada zumunta wanda a zamanan ce harkar kwallon kafa ta zama hanyar samar da aikin yi ga matasa da kuma bunkasa tattalin arziki na kasa.

Ya kara da cewar hukumar ta shirya wannan wasan kwallon kafa ne domin nuna wa shugaban kasa Bola Ahmed tunubu goyon bayansu ga gwamnatinsa.

Daganan sai ya bayyana cewar wannan wasan ya kunshi jihohi bakwai na Arewa maso yammacin kasarnan ciki har da jihar kano.

Mataimakin gwamnan a madadin gwamnan jihar kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci ayarin hukumar wasannin zuwa filin wasa na marigayi janar sani Abacha inda aka gudanar da wasan.

Alhaji murtala sule Garo jim kadan da kammala wasan ya gabatar da jawabi inda ya bayyana cewar wasan kwallon kafa yana hada kan alumma saboda ya kunshi kabilu daban daban na kasarnan kuma yana sadar da zumunci sannan kuma hanya ce bunkasa rayuwar matasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Majalisar Dokokin Kano Tayi Kira Kan Gaggauta Hukunta Wadanda Suka Kashe ‘Yan Arewa A Jihar Edo

Daga: Muhammad Adamu Abubakar Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kiran da a…

Gwamnatin Jihar Nan Ta Jajantawa ‘Yan Kasuwar Farm Centre Bisa Ibtila’in Gobara

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi A martanin da mai girma mataimakin gwamnan jihar…

Gwamnonin Arewa Sun Fara Daukar Sabbin Matakai Don Tunkarar Ta’addanci

Daga: Sani Idris Maiwaya A kokarinsu na fuskantar matsalar tsaro da ta…

Kungiyar ‘Yan Jarida Ta Kasa Reshen Gidan Rediyon Tarayya Pyramid Za Ta Kulla Alaka Da Kamfanoni Domin Cigaba

Daga: Muhammad Adamu Abubakar  Shugaban kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Gidan Rediyon…