Daga: Saminu Ibrahim Magashi
A wani mataki na nuna jinkai da kula da marasa galihu, gidauniyoyin FAYU da MAITUWU sun shirya wani gagarumin taro a jihar Kano domin tallafawa yaran da gwamnati ta ceto daga rayuwar gararamba a kan tituna.
Taron wanda aka gudanar a Makarantar Kwana ta WTC, ya mayar da hankali ne wajen saka wa yaran farin ciki tare da nuna musu cewa suma suna da matsayi a cikin al’umma kamar kowane yaro.
Da take jawabi, shugabar ɗaya daga cikin gidauniyoyin, Hajiya Uwani Ahamda Balarabe, ta bayyana cewa manufar shirin ita ce ƙarfafa gwiwar yaran tare da nuna musu kulawa da ƙauna. Ta ce kamar yadda ake shirya wa ‘ya’ya shakatawa a lokutan bukukuwa, haka ma waɗannan yara suka cancanci jin daɗi da kulawa ta musamman.

A nata ɓangaren, wakiliyar uwargidan gwamnan jihar Kano, Hajiya Sadiya Abdu Bichi, ta jaddada ƙudirin gwamnatin jihar na ci gaba da kula da rayuwar jama’a, musamman yaran da aka ceto daga kan tituna.
Ta bayyana cewa gwamnati na ci gaba da horar da yaran kan sana’o’i daban-daban, tare da ba su ilimin addini da na boko, domin su zama masu amfani a gaba. Ta kuma tabbatar da cewa gwamnati a shirye take ta ci gaba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyin agaji wajen tallafawa marayu da marasa galihu.
An gudanar da taron ne tare da halartar manyan baƙi ciki har da wakilin Hakimin Dawakin Kudu, Sakatare a Ma’aikatar Tarihi da Al’adu ta jihar Kano, Alhaji Abba, malamai, ɗalibai da sauran jama’a.

An kuma gudanar da wasanni da nishaɗi daban-daban domin ƙara wa yaran farin ciki da walwala.