Daga: Musa Mudi Dawakin Tofa

Daga Masallacin Abdullahi Bin Umar unguwar Arziki mazabar Dawaki Yamma a karamar hukumar Dawakin Tofa dake jihar Kano, an gabatar da taron Daura (Bita) ta kwana daya a kan ilimin Akida, a ranar Lahadi 20/11/1446 (18/05/2025).
Farfesa Muhammad Muslim Ibrahim ne ya gabatar da daurar a inda ya yi amfani da littafin “Mujmal Usulul Ahlusunna Wal Ja’ama Fil Akida” (Dunkulallun Ginshikai a Cikin Akidar Mabiya Tafarkin Sunna) wallafar Doktur Nasiru Bin Abdulkarim Al’akil.

Farfesa Muslim, a yayin daurar ya karanta tare yin bayani daga cikin littafin dalla-dalla a game manya da kananan batutuwa ginshikai da ya kyautu duk wani mabiyin tafarkin sunnar Annabi Salallahu Alaihi Wasallama ya sansu, ya kudurcesu kana ya yi koyi da su a maganganunsa da kuma aiyukansa domin neman tsira daga wurin Allah madaukakin Sarki.
Daga karshe Farfesa Muslim Ibrahim, ya yi dogon jawabi tare da kira ga mahalarta Daurar a game hadin kan musulmi da kaucewa rarrabuwa a kan sabani na fahimta a tsakaninsu da kuma kiran alumma a kan haka.

An fara gabatar da taron Daurar daga 11:00 Na Safe zuwa 06:30 Na Yamma, manyan malamai da daliban ilimi maza da mata daga ciki da wajen karamar hukumar ne suka halarci taron Daurar a karkashin jagorancin shugaban Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah JIBWIS reshen karamar Dawakin Tofa, jihar Kano, Nigeria Malam Mustapha Sani.