Daga: Ibrabim Sani Gama

Kungiyar Kwankwasiyya Singa Market ta shawarci al’ummar kasuwar da su yi watsi da wata sanarwar kungiya a kasuwar ta fitar na cewar, ‘yan kasuwar kar su fito domin yin kasuwancinsu ranar lahadi saboda sun shirya yin gangamin sharar kasuwar.”

Shugaban kungiyar Alhaji Liti Kwasamgwami ne ya sanar da haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ofishin kungiyar dake kasuwar.

Liti Kwasamgwami yace wannan sanarwar da suka fitar Bata da tushe balantana makama a Don haka yake sanar da al’ummar kasuwar ta singa da su fito domin gudanar kasuwancinsu kamar yadda suka Saba a koda yaushe.

Shugaban kungiyar ya kuma yabawa Gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf bisa yadda yayi kokari domin ganin Mahajjatan Kano sun gudanar da aikin hajjinsu lafiya.

Yace Gwamnan jihar Kano injiniya Abba Kabir Yusuf ya taka mahimmiyar rawa ta fan in taimakawa alhazan jihar Kano da tallafin kudade da Samar musu da ingantaccen matsuguni yayin gudanar da ibadarsu Wanda kuma suka Yi ta cikin kwanciyar hankali da lumana.

Shugaban kungiyar Alh Liti Kwasamgwami yayi Kira ga Gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf daya waiwayi kungiyar kwankwasiyya singa market bisa gudunmawar da take baiwa ci gaban gwamnatin musamma yadda wasu mutane suke ganin kamar sun tura mota ta bulesu da hayaki.

Daga karshe shugaban kungiyar Alh Liti Kwasamgwami yace tunawa da kungiyar zai taimakawa kungiyar wajen fita daga cikin kalubalen yan adawa dake kokarin sare mata gwiwa da gatari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

ANPP Na Bukatar Kujerar Mataimakin Shugaban Ƙasa: Shin APC Zata Fuskanci Barazana ne?

Daga: Yakubu Abubakar Gwagwarwa Masana harkokin siyasa na bayyana cewa jam’iyyar APC…

Silar Karancin Gandaye Wannan Azumin – Hisbah

Daga: Jamila Suleiman Aliyu  Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yabawa iyaye da…

Kotu Ta Tabbatar Da Shugabancin David Mark A ADC

Daga: Abdullahi Bashir Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta tabbatar da…

Kotun Bebeji Ta Gurfanar da Mutane Biyu Kan Sayar da Naman Wata Saniya

Daga: Dantala Uba Nuhu Kura Kotun Majistare mai Daraja ta Ɗaya da…