Daga: Ibrahim Sani Gama

Kungiyar tsoffafin Daliban tsangayar makarantar Gwani sabiu dake Karamar Hukumar kura ta bukaci Gwamnatoci a matakai daban daban da sauran masu hannu da shuni da tsoffafin Daliban tsangayar,da su kasance masu tunawa da tsangayar duba da gudunmawar da take bayarwa na tsawan shekaru sama da tamanin.

Shugaban kwamatin Dattawan kungiyar Alh salisu Biliya Takai ne ya bukaci hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a lokacin taron tsaffin Daliban tsangayar na cikarta shekaru tamanin da kafuwa.

Alh salisu Biliya Takai yace, makasudun gudanar da wannan taro na wannan shekara shine, domin janyo hankalin mahukunta da sauran masu hannu da shuni da tsoffafin Daliban da suka koyi karatu a tsangayar da su rika waiwayar makarantar domin taimaka mata da Kara ingantata.

Salisu Biliya Takai ya bayyana cewar,yanzu haka akwai dalibai da dama da suke jihohin kasar Nan da kasashen ketare har zuwa jami’ar Madina Wadanda makarantar ce ta yayesu.

A jawabinsa Gwani Dr. Jafar kura Wanda kuma malami ne a jami’ar Yusuf maitama sule yayi Kira ga matasa da su jajirce wajen neman ilimi musamma na karatun Alkur”ani maigirma da sauran littafan addini domin sanin kansu a rayuwarsu ta yau da kullum da kaucewa shaye shayen muggwan kwayoyi da fadan daba da kwacen wayoyin alummar,Wanda sau da yawa rashin ilimi Yana taka gagarumar gudunmawa.

Malam surakatu sabiu kura Wanda daya ne daga cikin “ya”yan malam sabiu kura daya Samar da wannan makaranta ya bayyana cewar, tsangayar tana bukatar Samar mata da guraren kwanan Dalibai saboda ya yiwa tsangayar kadan Wanda akwai bukatar kawowa makarantar dauki domin ta ci gaba da habaka da ilimantar da alumma sanin karatun Alkur”ani maigirma.

A nasa bangaren Gwani saidu sabiu kura yayi Kira ga alumma da su jajirce wajen sada zumunci tsakanin alumma Wanda haka Yana kawo daukaka da bunkasar Arziki da tsawan rai ga duk Wadanda suke sada zumunci tsakaninsu.

Haka zalika Gwani saidu sabiu kura ya yabawa Wadanda suka assasa wannan kungiya Wanda ya bayyana cewar,yin hakan zai taimaka gaya wajen sada zumunci tsakanin juna da yawan tunawa da marigayi Malam Sabi’u Kura daya samar da wannan tsangaya shekaru sama da tamanin da suka gabata.

Daga karshe ya shawarci dukkannin tsaffin Daliban tsangayar da ma Wadanda suke makarantar har yanzu,da su zo a Kara hada hannu da karfe domin ci gaba assasa wannan kungiya da ita kanta tsangayar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Inganta Ilimin Yara Shine Burinmu

  Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa Hukumar Nan dake wayar dakan Jama,a…

Tagomashin Bada Ilimin Gaba da Digiri a Fannin Koyarwa – Ayuba

Daga: Jamila Suleiman Aliyu Makarantar Kwalejin Koyarwa ta Aminu Kano (AKCOE) hadin…

Zulum Ya Kaddamar Da Gina Manyan Makarantu Guda Biyu A Hawul

Daga: Kabir Getso Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya fara aikin…

Hisbah Ta Jagoraci Wa’azi Ga Mata

Daga: Jamila Suleiman Aliyu  Hukumar Hisbah ta karamar hukumar Tarauni ta shirya wa’azi…