Daga: Jamila Suleiman Aliyu 

Hukumar Hisbah ta karamar hukumar Tarauni ta shirya wa’azi ga mata domin nusar dasu irin romon dake cikin watan Ramadan mai albarka, wanda suka gabatar a yankin cikin makarantar firamare ta darmanawa dake karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.

Kwamandar mata a Hisbah ta karamar hukumar Tarauni Malama Maryam Ibrahim Kanti ita ce ta jagoranci gabatar da wa’azi, a inda ta bayyana cewa, falalar da watan yake da ita ba zai misaltuba. Don haka ta ja hankalin matan yankin da su dage su samu falalar da ke cikin wannan watan mai albarka duba da yadda ake rabauta da ‘yan uwa daga wuta, gafara daga zunubai da kuma falalar samun Aljanna inda ta bayyana cewar Manzoni tsira S. A. W yace “ku kubutar da kawukanku daga wuta koda da tsagin dabino ne`don haka ta ja hankalin matan dasu taimakawa juna kuma karsu raina abin da zasu bayar sadaka musamman a wannan lokacin.

Malama Maryam, ta kuma bayyana yadda kissar munbarin Annabi ta samo asali inda tace wata sahabiya ce ta umarci danta kafinta ya sassakawa ma’aiki munbarin kuma yabi umarnnin mahaifiyarsa ya sassaka munbarin kuma ta bayyana cewa munbarin yana da matattakala uku inda kuma a yayin taka ko wace matattakala ta wannan mumbarin sai akaji Manzon Allah yana cewa “Ameen Ameen Ameen” sai sahabbai suka tambayi Annabin cewa munji kana cewa Ameen Ameen Ameen sai annabi yace 1. Ameen ta farko mala’ika Jibril yace ka ce duk wanda ya rayu da Iyayensa baiyi aikin da zai kaishi Aljanna ba in ya shiga wuta ya dannashi a kasan ta sai Annabi yace Ameen kuma duk wanda aka ambaci Annabi baice Ameen ba shima in ya shiga wutar a dannashi a kasan ta sai Annabi ya ce Ameen 3. kuma duk wanda Ramadana ya zo ya wuce baiyi abinda za’a gafarta masa ba shima inya shiga wutar a dannashi kasan ta sai Annabi yace Ameen.

Malama ta ja hankali matuka akan bin iyaye inda ta kara musu bayani akan su bi mazajen su yadda ya kamata kuma su rubanya a wannan watan na Ramadan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Tsangayar Mal. Sabi’u Kura ta Kai Sama Da Shekaru Tamanin Da Kafuwa

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar tsoffafin Daliban tsangayar makarantar Gwani sabiu dake…

Tagomashin Bada Ilimin Gaba da Digiri a Fannin Koyarwa – Ayuba

Daga: Jamila Suleiman Aliyu Makarantar Kwalejin Koyarwa ta Aminu Kano (AKCOE) hadin…

Silar Karancin Gandaye Wannan Azumin – Hisbah

Daga: Jamila Suleiman Aliyu  Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yabawa iyaye da…

Ya Zama wajibi Mu yabawa Hajiya Halima Muhammad Nuhu…… Dagacin Riga Fada Alhaji Shuaibu Madaki

Ya Zama wajibi Mu yabawa Hajiya Halima Muhammad Nuhu…… Dagacin Riga Fada…