Daga: Mas’ud Mato Garo

Shugaban Karamar Hukumar Kabo, Comr. Lawan Najume Kabo, ya jagoranci raba takardun daukar aikin koyarwa ga malamai 120 da Gwamnatin Jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta baiwa ‘yan karamar hukumar Kabo a yau Litinin, inda aka baiwa kowanne malami tallafin Naira Dubu Ashirin domin kudin mota.

A taron rabon takardun da aka gudanar a sakatariyar karamar hukumar, Shugaban ya bayyana cewa wannan mataki na gwamnati na da nufin inganta fannin ilimi da rage rashin aikin yi a yankin. Ya ce an zabi malaman ne daga cikin ‘yan asalin karamar hukumar bisa cancanta, kuma za su fara aiki nan take a makarantun firamare da sakandare dake fadin karamar hukumar.

Comr. Najume ya kara da cewa kudi N20,000 da aka baiwa kowane malami tallafi ne domin sauwaka musu halin tafiya zuwa makarantun da aka tura su. Haka zalika, ya bukaci sabbin malaman da su yi aiki tukuru, cikin gaskiya da amana domin ganin sun sauke amanar da gwamnati ta dora musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

‘Yan Bindiga Sun Sace Mamallakin Jaridar Rariya

‘Yan Bindiga Sun Tare Mamallakin Jarida Rariya Sani Ahmad Zangina A Hanyar…

Dandazon al’umma sun tarbi gwamnan Kano biyo bayan dawowarsa daga kasa Mai tsarki

Daga: Adamu Dabo   A yau laraba dubban al’ummar jihar Kano daga…

Gwamnatin Sakkwato: Ba Za’a Yi Sulhu Da Turji Ba Sai Ya Sako Wadanda Ya Yi Garkuwa Da Su

Daga: Sani Idris Maiwaya Gwamnatin Jihar Sakkwato ta bukaci shugaban ’yan bindiga, Bello…

Dawowar Abba Kabir Yusuf APC Zai Haifar Da ‘Da Mai Ido A Kano – Tumfafi

Daga: Ibrahim Sani Gama Sakataren Kungiyar Kasuwar Abinci ta Duniya da ke…