Daga: Dantala Uba Nuhu Kura

Kotun Majistare mai Daraja ta Ɗaya da ke ƙaramar hukumar Kura, a jihar Kano, ta gurfanar da wani matashi bisa zargin sare yatsan hannun wani matashi mai suna Abubakar Abba.

An gurfanar da wanda ake zargin ne a gaban kotu bayan da mai gabatar da ƙara, Insifecta Nasiru Abubakar Dan-Sakkwato, ya karanta takardar tuhumar da ke kunshe da zargin aikata laifin sare yatsan hannun Abubakar Abba.

Bayan karanta tuhumar, wanda ake zargin ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa, inda ya bayyana rashin amincewa da zargin gaba ɗaya.

Nan take, Alkalin Kotun Majistare mai Daraja ta Ɗaya ya ɗaga sauraron shari’ar zuwa ranar 18 ga watan Janairu, 2026, domin ci gaba da shari’ar.

Alkalin kotun ya kuma bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a hannun jami’an gidan ajiya da gyaran hali, ƙarƙashin kulawar Insifecta Awwalu Muhammad Danhasan, har zuwa ranar da za a ci gaba da shari’ar.

Bayan fitowar daga kotu, wakilinmu, Dantala Uba Nuhu Kura, ya samu tattaunawa da wanda aka sarewa yatsan hannu, Abubakar Abba, inda ya bayyana abin da ya faru, yana mai roƙon a yi masa adalci a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Shaye-Shaye: Al’ummar Rimin Kebe Sun Bukaci A Kawo Musu Dauki

Daga: Mukhtat Yahaya Shehu Kungiyar ci gaban matasan unguwar Rimin Kebe Karshen Kwalta…

Gwamna Abba Ya Amince Da Nadin Amirul Hajj Na Kano

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince…

Bawa Mata Dama A Siyasa Shine Ginshikin Cigaban Al’umma

Daga: Kabir Getso Tsohuwar Babbar Daraktan Hukumar Kula da ‘yancin Mata ta Jihar…

Zamu Kashe Sama da Naira Miliyan 87 Dan Sanya Interlock a Sakatariyar Karamar Hukumar Dala Da Kuma Wasu Gyare Gyare a Cikin Karamar Hukumar

Daga: Sani Idris Maiwaya Gwamnatin jihar Kano ta amince da kashe sama…