Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da nadin Sarkin Gaya, Alhaji Dr. Aliyu Ibrahim Abdulkadir, a matsayin Amirul Hajj na jihar domin jagorantar aikin Hajjin shekarar 2026.

Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Muhammad Maharaz, an nada shi a matsayin Mataimakin Amirul Hajj.

Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana sa ran Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano za ta bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Amirul Hajj da mataimakinsa domin tabbatar da gudanar da aikin Hajjin cikin nasara da kwanciyar hankali.

Haka kuma gwamnatin ta yi wa Amirul Hajjin da mataimakinsa da ma’aikatan Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar fatan alheri tare da addu’ar Allah ya ba maniyyatan jihar damar gudanar da aikin Hajji karbabbe tare da dawowa gida lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Najeriya Tayi Nasara Akan Benin 4-0, Tana Shirin Samun Gurbin Gasar Cin Kofin Duniya

Daga: Kabir Getso A cikin wasan ban sha’awa da aka yi a Filin…

Garo Ya Kama Aiki, Ya Yi Alkawarin Adalci Da Kyakkyawan Jagoranci

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Sabon mataimakin gwamnan jihar Kano, Alhaji Murtala Sule…

KNHA, JIBAL Sun Horas Da ’Yan Jarida Kan Rahotannin Majalisa

Daga: Muhammad Adamu Abubakar Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano (KNHA), RT. Hon.…

Ma’aikatar Jinkai ta Kano Ta Raba Tallafin Abinci Ga Jama’a, Tare da Kai Ziyara Ga Masu Bukata Ta Musamman

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa A ci gaba da kokarinta na rage wa…