Daga: Mukhtat Yahaya Shehu
Kungiyar ci gaban matasan unguwar Rimin Kebe Karshen Kwalta da ke Karamar Hukumar Ungogo ta koka da yadda wasu matasa a Yankunan suke Kasuwancin mugayen kwayoyi da tabar wiwi da zama a wani fili dake Unguwar, wanda hakan yana kawo barazana ga lafiya da dukiyoyin al’ummar Yankunan.
Shugabannin kungiyar matasan unguwar madadin al’ummar yankunan Danlami Kabiru da Abdulrahaman Bello ne suka yi koken a lokacin da suka yi taron manema labarai dangane da halin da jama’ar unguwar suke ciki.
Danlami Kabiru ya bayyana cewa cinikin Muggan Kwayoyi ya zama ruwan dare duk da cewa yanzu lokacin watan azumi ne, amma matasan basa daga kafa wajen shaye-shaye da kasuwancin muggwan kwayoyi.
Ya ce, dangane da haka kungiyar matasan yankin ta shirya taron manema labarai domin sanar da gwamnati da sauran mahukunta da masu ruwa da tsaki da hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da su shigo domin tallafawa al’ummar wannan yanki duba da halin suka samu kansu a ciki.
Danlami Kabiru ya kara da cewar, a kwanakin baya kungiyar matasan ta gudanar da taro da masu zama a filin da ake shaye-shayen tare yin kira a garesu da su dakatar da zaman da suke yi a wannan wuri, inda suka dauki alkawarin ba za su kara zama a filin ba, amma daga bisani suka dawo tare da ci gaba da harkokinsu na kasuwancin muggan kwayoyi da tabar wiwi da zama shaye-shaye.
Abdulrahaman Bello, ya yi kira al’ummar Yankunan na Rimin Kebe Karshen Kwalta da masu ruwa da tsaki da masu hannu da shuni da taimako wajen yakar wannan mummunar dabi’ar da wasu daga cikin matasan unguwar ta Rimin Kebe Karshen Kwalta suke a wannan fili. Bugu da kari Kungiyar ta kuma bukaci mamallakin filin da ake yin wannan ta’asar dake layin Sule Dankano da ya zo ya gia shi domin a samu damar dakatar da abubuwan da ake yi a filin wanda yanzu haka mata ma sun fara daukar wannan dabi’a. Daga karshe kungiyar ci gaban unguwar ya yi kira mai unguwa Malam Miko da ya taimakawa Kungiyoyin Yankunan domin tallafawa na kawo Karshen Kasuwancin Muggan Kwayoyi da tabar wiwi da zama shaye-shaye a Unguwar Rimin Kebe Karshen Kwalta.