Daga: Ibrahim Sani Gama
Kungiyar Jami’an Tsaro na Sa Kai ta Kasa reshen jihar Kano ta bayyana kudirinta na ci gaba da samar da cikakken tsaro a dukkanin fadin kasar nan, tare da bukatar a sanya su cikin tsarin biyan albashi na dindindin.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Jami’in Hulda da Jama’a na kungiyar, S. A. Usman Abdullahi Umar, yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsu dake Kano.

Ya ce kungiyar na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da tsaro ba kawai a jihar Kano ba, har ma da sauran sassan Najeriya, karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Alhaji Abdullahi Al’amin.
“Ayyukan da jami’anmu ke yi a fadin kasar nan sun fi karfin yabawa. Muna buƙatar goyon baya daga gwamnati domin inganta wannan gudummawa,” in ji shi.

Ya jaddada cewa lokaci ya yi da gwamnatin tarayya da na jihohi za su duba yiwuwar sanya jami’an tsaro na sa kai cikin tsarin biyan albashi, domin hakan zai ba su damar dogaro da kansu da kuma tallafa wa iyalansu.
A cewarsa, “Yanzu haka jami’anmu suna aiki ne da ƙarfin gwiwa wajen yaki da laifukan da ke addabar al’umma, musamman kwacen waya da matasa ke yi wanda ya zama barazana ga rayuwar jama’a.”
Usman Umar ya kara da cewa kungiyar na gudanar da ayyukanta da kadan daga cikin abinda take da shi, lamarin da ya sa ya bukaci gwamnatin tarayya da ta jihohi su tallafa musu da kayayyakin aiki da kudaden gudanarwa.
“Idan gwamnati ta sanya mu cikin tsarin albashi, kamar yadda ake yi wa sauran jami’an tsaro, hakan zai taimaka matuka wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma,” in ji shi.
Ya kuma shawarce su da su kasance masu biyayya ga dokokin kungiyar, tare da kare hakkokin wadanda ake zalunta.
“Kungiyar ba za ta lamunci cin zarafin al’umma daga wani jami’in sa kai ba. Dole ne mu kasance masu kare gaskiya da adalci,” in ji shi.
A karshe, ya yi kira ga dukkan jami’an sa kai da su kara zage damtse wajen gudanar da aikinsu da gaskiya da rikon amana. Haka kuma ya basu tabbacin cewa shugabannin kungiyar a matakin kasa na ci gaba da kokarin ganin an sanya su a cikin tsarin biyan albashi da kayayyakin aiki da sauran hakkoki.