Daga: Zakariyya Adam Jigirya
Abuja – A wani babban taron da ya samu halartar manyan jami’ai da ‘yan kasa daga sassa daban-daban, Shugaban Kwamitin Gidaje da Muhalli na Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Abdulmumin Jibrin Kofa, wanda kuma shine Jarman Bebeji, tare da Manajan Darakta na Hukumar Kula da Gidaje ta Najeriya (FHA), Oyetunde Ojo, sun kaddamar da wani sabon rukunin gidaje na zamani mai suna FHA Airport Express View Estate da ke kusa da hanyar filin jirgin sama a babban birnin tarayya, Abuja.

An gudanar da bikin kaddamarwar ne a ranar Juma’a, inda aka bayyana cewa wannan aiki wani muhimmin ci gaba ne a kokarin gwamnatin tarayya na samar da gidaje masu inganci ga ‘yan Najeriya, musamman ma a manyan birane kamar Abuja. Rukunin gidajen na da nufin rage gibin rashin gidaje da ake fama da shi a fadin kasar nan, tare da inganta rayuwar jama’a.
A jawabinsa yayin kaddamarwar, Hon. Abdulmumin Jibrin ya bayyana gamsuwarsa da yadda aka tsara aikin cikin kwarewa da kuma ganin an samu ingantaccen sakamako da zai amfani al’umma. Ya ce:
“Wannan rukunin gidaje ba wai kawai zai taimaka wajen samar da matsuguni bane, har ma da nuna muhimmanci wajen bunkasa tattalin arziki, samar da ayyukan yi da kuma janyo jarin ‘yan kasuwa masu zaman kansu cikin harkar gine-gine da gidaje.”
Shi ma a nasa bangaren, Manajan Darakta na FHA, Oyetunde Ojo, ya bayyana cewa an tsara rukunin gidajen ne da fasahar zamani, tare da tanadin ababen more rayuwa da suka hada da hanyoyi masu kyau, ruwan sha, wutar lantarki da tsaro. Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da yin hadin gwiwa da masu zuba jari domin samar da karin gidaje a sassan kasar nan.
Rukunin gidajen da aka kaddamar yana daya daga cikin ayyukan da hukumar FHA ke aiwatarwa karkashin sabon tsarin raya kasa da kuma kudirin gwamnatin tarayya na samar da gidaje miliyan daya (1,000,000) a matakin kasa.

Bikin ya samu halartar wasu ‘yan majalisar wakilai, shugabannin hukumomi, ‘yan kasuwa, da kuma wakilan kungiyoyin kwadago da na fararen hula, wadanda duk suka yaba da kokarin gwamnati da kuma irin jajircewar da Hon. Jibrin Kofa da shugabannin FHA ke nunawa.
Ana sa ran za a ci gaba da irin wannan aikin a sauran manyan biranen kasar, domin tabbatar da cewa kowanne dan Najeriya yana da damar mallakar gida mai inganci da saukin samu.
