Daga: Nura Garba Jibrin

Kungiyar ‘Yan Kasuwa da Masu Safarar Ridi ta kasa, reshen Jihar Kano, ta yi gargadin cewa matsalolin tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Arewacin Najeriya na iya kawo ƙarshen noman Ridi a yankin.

Shugaban kungiyar a Kano, wanda kuma sanannen ɗan kasuwa ne a kasuwar Dawanau, Alhaji Ibrahim Muhammad Dawanau, da aka fi sani da Danliti Y.Y, ya bayyana haka a wata tattaunawa da wakilinmu.

Ya ce, hare-haren tsaro a jihohin Borno, Zamfara, Katsina, Sokoto da Yobe na daga cikin manyan barazanar da ke gurgunta harkar noman Ridi, inda ya bukaci gwamnati ta dauki matakan gaggawa don dakile wannan matsala.

Baya ga tsaro, Danliti ya ce, rashin kayan aikin zamani na noma, irin su taraktoci, ingantattun iri da kuma magungunan kashe kwari, na daga cikin manyan kalubale da manoman Ridi ke fuskanta.

“Idan gwamnati za ta sauƙaƙa samun takin zamani, taraktoci, da ingantattun iri, ni kaɗai zan iya noma sama da hekta 100. Amma a halin yanzu ko hekta 30 ma ba zan iya nomawa ba,” inji shi.

Ya bukaci gwamnatin tarayya, jihohi da kuma kananan hukumomi da su hada kai wajen samar da hanyoyin da za su farfado da harkar noman Ridi a kasar.

A nasa bangaren, mataimakin shugaban kungiyar, Malam Babangida Mansur, ya jinjinawa gwamnatin Jihar Kano, musamman kwamishinan kasuwanci, bisa matakan da take dauka wajen bunkasa kasuwar Dawanau.

Mansur ya jaddada cewa akwai bukatar gwamnati ta kara mayar da hankali wajen horar da ‘yan kasuwa kan dabarun amfani da lamunin da ake basu daga gwamnati da kungiyoyin duniya. Ya kuma bukaci samar da jarin da ba ya ɗauke da riba domin karfafa kasuwanci, wanda zai taimaka wajen habaka tattalin arzikin jihar da kuma samar da ayyukan yi.

Haka kuma ya yi kira ga kungiyoyin ‘yan kasuwa da su kara hada kai wajen samar da hanyoyin ci gaba da zai amfani dukkanin mambobinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamna

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Majalisar dokokin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta fara…

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) Ta Musanta Zarge-Zargen Ƙarya da Ƙazafi

Daga: Abba Bashir Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta jawo hankalin jama’a dangane…

Gwamna Abba Ya Amince Da Nadin Amirul Hajj Na Kano

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince…

Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Sake Jaddada Muhimmancin Noman Lambun Gida Bayan Girbi

Daga: Abdullahi Bashir Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta sake girbe kayan…