Daga: Abba Bashir

Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta jawo hankalin jama’a dangane da wasu rahotanni na ƙarya da ke yawo a kafafen yaɗa labarai da ake zargin cewa, an kashe sama da Naira Biliyan 1.64 wajen ɗaukar nauyin iyalan ma’aikata a aikin Hajjin bana 2025. Daga cikin waɗannan zarge-zarge har da ikirarin da ba su da tushe, cewa, Shugaban Hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sauka a dakin haya mai darajar $1,000 a kowacce rana dake Otel din Hilton Makkah Suites tare da kai wasu ‘yan uwansa 12. NAHCON ta bayyana cewa waɗannan zarge-zarge ba su da wata hujja kuma suna nuna wani yunkuri ne na ɓata suna da tunzura jama’a.

Domin fayyace gaskiya, NAHCON ta jaddada cewa, ba ta ɗaukar nauyin tafiya ko masaukin matan ma’aikata. Abin da ke akwai shi ne, tsarin walwala da Hukumar ta amince da shi, wanda ke baiwa ma’aikatan da suka yi fiye da wata ɗaya a Saudiyya damar ɗaukar matansu a ƙaramin farashi duk da cewa wannan tsari ba ya haɗe da muhimman abubuwa kamar masauki a Makka, abinci, kuɗin tafiya (BTA), da jigilar cikin birane. Waɗannan duk nauyin da ma’aikacin da ya ɗauki matarsa ke ɗauka daga aljihunsa ne.

Zargin cewa ma’aikatan NAHCON ba su da kuɗin ɗaukar nauyin matansu babban ƙarya ne kuma ya tabbatar da raini. Wannan shiri na zaɓi ne, ba tilas ba. A wasu lokuta ma, matan su ke taimakawa wajen ɗaukar kuɗin tafiyarsu. Babu wani keta doka ko ɓarna a cikin wannan tsari mai gaskiya da ke bayyane.

Adadin kuɗaɗen da ake yadawa a cikin rahotannin ƙarya an gina su ne bisa kuskuren fahimta. Akasin abin da ake ikirari, wannan tsari na tallafi ga matan ma’aikata bai wuce kuɗin biza, tikitin jirgi, da masauki a Masha’ir da Madina ba. Duk wani rahoto da ke cewa an biya fiye da haka ƙarya ne ba tare da wata shaida daga takardun hukuma ba.

Game da zargin da aka yi wa Shugaban Hukumar, NAHCON ta musanta zargin gaba ɗaya, tana cewa babu wata takarda ko bincike da ke nuna cewa an biya masa haya a ɗaki na alfarma ko tafiya da iyali bisa kuɗin gwamnati. Gaskiyar magana ita ce, Shugaban ya bi tsarin da ya dace wajen ɗaukar iyalansa da kuɗinsa, kuma babu wani ɗan uwansa da ya shiga aikin Hajji karkashin NAHCON. Har ma da biza, an yi ta ne ta hanya mai zaman kanta.

Hakanan, zargin cewa matan ma’aikata sun zauna a masaukin da aka tanada wa mahajjata ko jami’an gwamnati shima ƙarya ne. NAHCON na da tsari mai ƙarfi da ya tanadi kulawa daga ƙungiyoyi da aka ware domin tabbatar da cewa babu wani amfani da masauki ba bisa ƙa’ida ba.

NAHCON na maraba da kowanne irin bincike daga hukumomin da suka dace kamar EFCC, amma irin wannan bincike ya zama sai an dogara da gaskiya, ba ƙarya da anƙari don bita-da-kullin siyasa ba. Hukumar na fuskantar duba akwatunan kuɗinta a-kai-a-kai daga Ofishin Mai Duba Ƙididdiga na Ƙasa, kuma tana aiki bisa ka’idojin gaskiya da amana.

Abin takaici ne cewa, duk da nasarar da Hukumar ta samu a aikin Hajji na 2025 da ake yabawa a matsayin mafi nasara cikin kusan shekaru 15, har yanzu akwai waɗanda ke ƙoƙarin bata mata suna. Wasu daga cikin waɗannan na iya zama masu adawa da sauye-sauyen da aka kawo, ko rashin jin daɗi da jagorancin gaskiya, ko kuma tsoron halin da Shugaban hukumar ke da shi na amana da nagartaccen shugabanci na addini.

Daga ƙarshe, gaskiya za ta bayyana. NAHCON na nan daram bisa ayyukanta na gaskiya, amana da hidimar al’ummar Musulmai na Najeriya. Duk wanda ke ƙoƙarin hana cigaba ko rushe martabar wannan Hukuma saboda siyasa ko son rai, zai fuskanci faduwar gaba da gaskiya za ta tona masa asiri.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Remi Tinubu Ta Bukaci Burna Boy, Davido Da Asake Su Kafa Gidauniyoyi Don Taimaka Wa Talakawa

Daga: Sani Idris Maiwaya Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta yi kira…

Zamu Ci Gaba Da Baiwa Gwamnatin Jihar Kano Hadin Kai Domin Samar Da Tsaro Da Dakile Masu Kwacen Wayoyin Al’umma.

Daga: Ibrahim Sani Gama   Kungiyar ‘Yan Kasuwar Rimi da ke Jihar Kano…

Shugabannin Majalisa Sun Nuna Fargaba Kan Tsananin Ciwo Bashi da Rashin Sa Ido

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, tare da Shugaban…

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Taya Al’umar Musulmi Murnar Bikin Karamar Sallah 

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya…