Daga: Mukhtar Yahaya Shehu 

Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya Al’umar Musulmi murnar kammala Ibadar Azumin Ramadana tare da murnar bikin sallah karama.

“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da jiha da Kana Nan Hukumomi da su mayar da hankali domin kare rayuka, Lafiya da Dukiyoyin Al’uma”. – Sarki Kano Alhaji Aminu Ado Bayero.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya yi wannan kira ne a lokacin da yake gabatar da Jawabinsa na Barka da Sallah Jim kadan da idar da sallah Idi Karama a fadarsa dake Gidan Sarki na Nassarawa a birnin Kano.

Cikin sanarwa Mai dauke da sa hannun mai magana da yawun fadar Sarki Abubakar Balarabe Kofar Na’isa ta ce ya Zama wajibi shugabanni su yi la’akari da yanayin rayuwa da Al’uma suke ciki akan abubuwan da sukafi bukata.

Sarkin ya bukaci su kasance masu yiwa Shugabanni addu’a da Kuma kyautata musu zato akan dukkanin al’amuran shugabancinsu.

Mai martaba sarkin ya yi addu’ar Allah Ya cigaba da Tabbatar da alheri tare da bawa shugabannin ikon aiwatar da abubawan da sukafi damun Al’uma Musamman harkar tsaro da saukin abinci da kayan masarufi.

Ya godewa Gwamnatin Tarayya da ‘Yan Majalisar Dattawa da na tarayya sa ‘yan Majalisun jiha bisa irin Taimakon da suka yi wa Jama’a a lokacin watan azumin Ramadan, inda ya yi fatan za su cigaba davirin wannan taimako.

Sarkin Kano ya godewa Malamai da Limamai bisa fadakarwa tareda kira Nan gaskiya da sukayi a lokacin azumi akan tafarki na gaskiya.

Kazalika Sarkin ya yaba wa ‘yan kasuwa da attajirai bisa gudumawa da suka bayar inda yayi fatan zasu cigaba da ganin kayan abinci dana masarufi sun cigaba dayin saukin ta yadda Al’uma zasu amfana.

Alhaji Aminu Ado Bayero daga nan ya taya Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da Jami’an Gwamnati da sauran Al’uma Muranar Barka da Sallah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Kwamitin Gawuna/Garo Kan Ayyuka Na Musamman Ya Ziyarci AA Zaura

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu Kwamitin Gawuna-Garo Strategic Project ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muhammad Badaru…

Mataimakin Gwamnan Kano, Gwarzo, Zai Cika Shekaru 65 da Haihuwa

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Mataimakin Gwamnan JiharKano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, zai…

An Wanke Shugaban Hukumar NAHCON Daga Zargin Nuna Son-Kai

Daga: Abba Bashir Kungiyar Cigaban Matasa Arewa ta Progressive Northern Youth (PNY) ta…

Iftar: Gwamnatin Kano Ba Za Ta Lamunci Cin Zarafi A Kafafen Yada Labarai Ba – Comrade Waiya

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu Gwamnatin jihar Kano ta yi alwashin hada hannu da…