Daga: Mukhtar Yahaya Shehu 
Kwamitin Gawuna-Garo Strategic Project ƙarƙashin jagorancin Alhaji Muhammad Badaru Umar Ungogo ya kai ziyara ga wanda ya yi wa Jam’iyyar APC Takarar Ɗan Majalisar Dattawa na Kano Ta Tsakiya, Alh. Abdussalam Abdulkarim (A.A Zaura), a ofishin sa dake Babban Birnin Tarayya Abuja.
Alhaji Muhammad Badaru ya ce ziyarar tana daga cikin ziyarce-ziyarce da kwamitin ke yi musamman ga manyan jiga-jigan jami’iyyar da wadanda suka yi mata takara.
Da ya ke jawabi Alhaji Abdulsalam A.A Zauran ya bayyana matuƙar godiyar sa da murna da wannan babbar ziyara tare da tabbatar da jaddada mubaya’ar sa ɗari bisa ɗari ga wannan tafiya ta Gawuna-Garo.
“A iya tunani na tunda duk nagarta da wata daraja da kuma gogewa kowacce iri ce da ake nema akwai ta a jikin Dr Nasiru Yusuf Gawuna kuma akwai ta a jikin Alhaji Murtala Sule Garo, don haka a iya tunani na kamata ya yi a ƙara basu dama.” In ji AA Zaura

Ya ƙara da cewa kamata ya yi a ce jami’iyyar APC ta sake ba su dama domin yi mata takara a nan gaba.
A ƙarshe yayi addu’ar fatan Allah Ya kauda duk wani mishkila da tarnaƙi da zai iya taɓa wannan tafiya ta Gawuna-Garo mai ɗumbun alkairai, Allah Ya kuma basu gagarumar nasara da sauran duk kujerun Jam’iyyar APC Ya ƙara zaunar da jihar mu da ƙasar mu lafiya da yalwar arziƙi.
