
Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana kudirin gwamnatin jihar na ganin cewa ayyukan ilimi a sabuwar makarantar Gaya Polytechnic da aka kafa ta fara aiki kafin nan da karshen shekarar nan.
Mataimakin Gwamnan ya bada wannan tabbacin ne a lokacin da yake karbar bakuncin Mai Martaba Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir Ibrahim da ‘yan majalisar Masarautar Gaya wadanda suka kai ziyarar Sallah.
Comr. Gwarzo, wanda kuma shine kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar, ya bayyana cewa gwamna Abba Kabir Yusuf ya umurci ma’aikatar sa da ta fara shirye-shiryen da suka dace na kwalejin kimiyya da fasaha.

Ya kara da cewa a halin yanzu sauran tsare-tsare na raya kasa da na dan Adam da na ababen more rayuwa suna gaban Gwamna Yusuf domin amincewa da aiwatar da su.
Mataimakin Gwamnan ya kuma bayyana cewa, ana ci gaba da shirye-shiryen raba wasu kaso na kudaden tallafi ga ‘yan fansho, wanda ya ce zai kara habaka tattalin arzikin Kano.
Da yake jawabi tun da farko, Sarkin Gaya, Alhaji Aliyu Abdulkadir Ibrahim, ya ce shi da ‘yan majalisarsa sun je gidan gwamnati ne domin tabbatar da al’adar da ta shafe fiye da karni guda ana gudanar da bukukuwan Sallah.
Sarkin ya yabawa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa manufofinta na dogaro da kai da kuma ayyukan da take gudanarwa a fadin jihar. Ya kuma yaba da kafuwar Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Gaya.
Yayin da yake yaba wa Gwamnan kan yadda ya magance matsalolin ruwa a Masarautarsa, Sarki Abdulkadir ya yi amfani da damar wajen yin kira ga gwamnati da ta magance matsalolin hanyoyin sadarwa a Masarautar sa.
Sarkin ya kuma mika ta’aziyya ga gwamnati da al’ummar Kano bisa mummunan rashin ‘yan wasa 22 da suka mutu a lokacin da suke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki na kasa da aka gudanar a Abeokuta, jihar Ogun.
A nasa martanin, mataimakin gwamna Gwarzo ya nuna jin dadinsa ga mai martaba sarkin da mukarrabansa bisa wannan ziyara da suka kai masa, ya kuma bada tabbacin cewa za a magance matsalolinsu da bukatunsu a lokacin da ya dace, domin samun maslaha.