Daga: Abdullahi Bashir

Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya sanar da kafa dokar ta-ɓaci ta awanni 48 a Ƙaramar Hukumar Jos North, bayan wani mummunan hari da ya auku a Angwan Rukuba.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne yayin da ya kai ziyara wurin da lamarin ya faru, inda ya bayyana cewa matakin na nufin dawo da doka da oda a yankin.

Ya kuma bai wa mazauna jihar tabbacin cewa za a gudanar da cikakken bincike domin gano waɗanda suka aikata harin tare da gurfanar da su a gaban kuliya.

Haka zalika, Mutfwang ya ce gwamnatin jihar za ta ɗauki nauyin jinyar waɗanda suka jikkata, tare da shirya jana’iza mai kyau ga waɗanda suka rasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

‎Al’ummar Jihar Borno Zasu Dade Suna Tuna Gwamna Zulum Bayan Wa’adinsa – ‎Hon Bundi

Daga: Kabir Getso Babban Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Borno Akan Kafafen Yaɗa…

Dalilan Da Yasa Gwamnatin Jihar Kano Ta Jaddada Aniyarta Na Ganin An Biya Diyyar Wadanda Aka Hallaka A Jihar Edo

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Wani babban kwamiti wanda gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba…

Babu Dalilin Rufe Kasuwar Singa Ranar Lahadi – Liti Kwasamgwami

Daga: Ibrabim Sani Gama Kungiyar Kwankwasiyya Singa Market ta shawarci al’ummar kasuwar da…

Jibrin Kofa Ya Jagoranci Kaddamar da Sabon Rukunin Gidaje a Abuja

Daga: Zakariyya Adam Jigirya Abuja – A wani babban taron da ya…