Daga: Ibrahim Sani Gama

Gwamnatin Jihar Kano ta samu gagarumar nasara a yaƙinta da magungunan jabu, inda aka kama magungunan bogi da ƙimarsu ta kai Naira biliyan 1.3, a wani samame da aka gudanar a Kanawa Pharmaceutical Coordinated Wholesale Centre (KPP-CWC), da ke cikin Kano Economic City, Dangoro, kan hanyar Zariya.
Babbar jami’ar harhaɗa magunguna a cibiyar, Hajiya Furera Ado Muhammed, ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar ranar a jiya Alhamis. Ta ce kamen ya biyo bayan tsauraran matakai da sahihan bincike da aka gudanar tun bayan rufe tsohuwar kasuwar magunguna da aka mayar da ita zuwa wannan sabon wurin na KPP-CWC.
A cewarta, bayan an yi gwajin ingancin samfuran magungunan, kusan kashi 40.3% sun gaza gwaji—musamman magungunan zazzabin cizon sauro, na kashe cututtuka da kuma na rage zafi da ake amfani da su wajen jinyar yara. Ta ce wannan na daga cikin manyan dalilan gazawar warkewa da kuma rasa rayuka da ake fuskanta.

Tuni dai aka miƙa magungunan da aka kama ga Kwamitin Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi na jihar domin a lalata su.
Hajiya Furera ta yaba da goyon bayan da hukumomin kula da harhaɗa magunguna irin su Pharmacy Council of Nigeria (PCN) da NAFDAC suka bayar. Ta kuma bukaci ƙarin wayar da kan jama’a domin tabbatar da bin ƙa’ida wajen harkar sayar da magunguna a jihar.
