
Daga: Shehu Suleiman Sharfadi
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da bayar da gudummawar Naira miliyan daya kowannensu ga iyalan ‘yan wasa 22 da suka rasa rayukansu a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a lokacin da suke dawowa daga gasar wasannin motsa jiki ta kasa.
Gwamnati ta kuma shirya raba kayan abinci da sauran kayan agaji don tallafawa iyalan wadanda abin ya shafa.
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya sanar da hakan a madadin gwamna Abba Kabir Yusuf a wata ziyarar jaje da ya kai asibitin Nasarawa inda aka ajiye gawarwakinsu.
Kwamared Gwarzo ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ba ga jihar Kano kadai ba har ma da daukacin al’ummar kasar baki daya. Ya yi nuni da cewa wadanda suka rasun matasa ne, ’yan wasa masu kishin kasa, wadanda suka wakilci jihar Kano.
Ya kara da cewa Gwamna Yusuf ya bayar da umarnin a gaggauta sakin tallafin kudi ga iyalai tare da ba da umarnin a samar da duk wani magani da ya dace ga wadanda suka tsira.

Ya kuma tabbatar wa da jama’a cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa iyalan wadanda abin ya shafa tare da kula da musibar da ta biyo baya cikin tausayawa da daukar nauyi.
Mataimakin gwamnan ya kuma ziyarci asibitin kwararru na Murtala Mohammed, inda ‘yan wasa bakwai da suka samu raunuka ke karbar kulawa domin jajanta musu.
