Daga: Jamila Suleiman Aliyu 

Gwamnatin Kano ta sha alwashin marawa matasa, masu bukata ta musamman, da yara wajen gina gobensu.

Kwamishinar mata, yara da masu bukata ta musamman Hajiya Amina Abdullahi Sani HOD ce ta bayyana hakan a yayin gagarumin bukin ranar mata da ya gudana a dakin taro na gidan Gwamnati wanda ta jagoranta tare da raba tallafin jari ga masu sana’o’i mabambanta da kuma baje kolin kayan sana’ar da aka koyarwa matasa.

Kwamishinar ta ce ba zatayi kasa a gwuiwa ba wajen zakulo wa mata hakkokinsu a duk inda suke don shine silar zuwan ta wannan kujera.

HOD ta kuma bayyana gwamnan Kano da jajirtacce a fannin daya shafi mata domin yana tsayawa tsayin daka a harkar matan duk da mai dakin gwamnan Sayyada mlMaryam Abba Kabiru tana cikin jerin matan da aka karrama da lambar yabo.

Haka zalika, Kwamishinar ta ce, ma’aikatarta zata waro matasa da zasu koyi sana’ar Gurasa a wurin wata kwararriya da aka karrama Malama Binta mai Gurasa don a samu yawaitar matasa a harkar gasa Gurasar don ci gaban jihar Kano baki daya.

Daga cikin matan da aka karrama sun hadar da uwa mai dakin tsohon shugaban kasa Hajiya Maryam Abacha da Hajiya Gaji Fatima Dantata da Hajiya Azumi Namadi Bebeji da sauran shahararrun mata a dai raba jari ga mata kimanin dari tara da tamanin da takwas.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Adeleke Ya Gode Wa Shugaba Tinubu Bayan Sake Zabarsa

Daga: Ibrahim Sani Gama Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya gode wa Shugaban…

Tinubu Ya Ce Hausawa Ginshiƙan Haɗin Kan Najeriya Da Ci Gabanta Ne

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana al’ummar Hausawa…

Zan Yi Amfani Da Shirin GEEP Don Inganta Rayuwar Matasan Nigeria – Hamza Ibrahim Baba

Hamza Ibrahim Baba ya kasance Shugaban hukumar kula da shirin gwamnatin tarayya…

An bayyana shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano kachima Dr. Rahila Aliyu Mukhtar amatsyin Mace wadda baza amance da ita ba a harkokin lafiya a jihar Kano.

An bayyana shugabar hukumar taimakekeniyar lafiya ta jihar Kano kachima Dr. Rahila…