Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana al’ummar Hausawa a matsayin manyan ginshiƙai wajen tabbatar da haɗin kan Najeriya da ci gabanta.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a yau Laraba, yayin da ake gudanar da bikin Ranar Hausa ta Duniya a fadar Mai Martaba Sarkin Daura, a Katsina.

Tinubu ya ce harshen Hausa ya samu gagarumin yaɗuwa, inda ya zama ɗaya daga cikin muhimman harsunan da ke taka rawa wajen haɗa kan al’umma da bunƙasa harkokin kasuwanci a Najeriya da sauran sassan duniya.

A cewar Shugaban Ƙasar, bikin Ranar Hausa wata dama ce ta nuna muhimmancin harshen da al’adun Hausawa wajen haɓaka haɗin kai da fahimtar juna tsakanin al’ummomin Najeriya da ma duniya baki ɗaya.

“Ina taya ɗaukacin al’ummar Hausawa murnar Ranar Hausa, wadda ake gudanar da bikin ta a yau a fadar Daura mai tarihi,” in ji shi.

Ana bikin Ranar Hausa ta Duniya, wato Ranar Hausa, a duk ranar 26 ga watan Agusta na kowace shekara, domin tunawa da muhimmancin harshen Hausa da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa wajen sadarwa da adana al’adu.

Harshen Hausa na daga cikin manyan harsunan da ake magana da su a Najeriya, kuma yana daga cikin harsunan da suka fi yaɗuwa a nahiyar Afirka.

Masana sun bayyana Hausa a matsayin ɗaya daga cikin muhimman harsunan Afirka, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa, ilimi, kafafen yaɗa labarai da harkokin kasuwanci a sassa da dama na nahiyar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Za Mu Ci Gaba da Tattara Kudaden Haraji – Shugaban ‘Yan kasuwar Tashar Malam Kato

Daga: Ibrahim Sani Gama KANO – Kungiyar ‘yan kasuwa dake tashar motoci…

Uwargidan Shugaban Ƙasa Ta Sake Jaddada Muhimmancin Noman Lambun Gida Bayan Girbi

Daga: Abdullahi Bashir Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta sake girbe kayan…

pin up brendinin Azərbaycan istifadəçiləri üçün tətbiq imkanları

pin up Azərbaycanda yükləmə və istifadə bələdçisi pin up brendinin Azərbaycan istifadəçiləri…

Masu Ruwa da Tsaki na Jam’iyyar APC a Madobi Sun Jaddada Goyon Bayansu ga Dukkan ‘Yan Takarar Jam’iyyar – Hassan

Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Karamar Hukumar Madobi sun…