Daga: Abdullahi Bashir

Wasu manyan shugabannin jam’iyyar ADC, ciki har da tsohon gwamnan jihar Anambra kuma tsohon dan takarar shugaban Ƙasar a shekarar 2023, Peter Obi, na nazarin yiwuwar ficewa daga jam’iyyar zuwa NDC gabanin babban zaɓen 2027.

Majiyoyi na kusa da Obi sun bayyana cewa wannan mataki na da nasaba da rashin gamsuwa da tsarin tafiyar da jam’iyyar ADC, tare da ƙarin rashin tabbas da ya biyo bayan hukuncin kotun koli.


Hukuncin kotun, wanda aka yanke a ranar Alhamis, duk da cewa wasu na kallonsa a matsayin sassauci na wucin gadi, ya ƙara jefa fargaba a zukatan shugabannin haɗakar siyasar gabanin zaɓen 2027.

Kotun kolin ta soke umarnin baya da ya cire David Mark da Rauf Aregbesola daga mukaman Shugaban Jam’iyya da Sakatare na ƙasa, sai dai hukuncin bai warware rikicin shugabanci gaba ɗaya ba, inda ta mayar da shari’ar zuwa babbar kotun tarayya domin ci gaba da sauraro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Tsadar Takin Zamani Ya Rage Cinikin Katifu a Arewacin Najeriya — Alh. Nasuru Abdulrahman

Daga: Ibrahim Sani Gama Kungiyar ‘yan kasuwar katifu a Jihar Kano ta…

An Yabawa Gwamnatin Kano Kan Sauya Sheƙa Cikin Lumana Zuwa APC

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Ambasada Suleiman Adamu ungogo ne ya furta hakan…

Zamu Dunga Gabatar Da Taron Hallara A Duk Lokacin Bikin Sallah

Daga: Abdulmajid Habib Isah Tukuntawa   Daga fadar Mai Martaba Sarkin Kano…

Asusun Tsaron Arewa: An Buƙaci Gwamnoni Su Mayar da Hankali Kan Aiwatar da Tsare-tsare

Daga: Abdullahi Bashir An bayyana cewa ƙaddamar da Hukumar Amintattu ta Asusun…