Daga: Bashir Abdullahi

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Dijital, Isa Pantami, ya yi watsi da matakin amincewa da Jamilu Gwamna a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Gombe gabanin zaben 2027.

Tun da farko a ranar Lahadi, Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya, ya jagoranci manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wajen bayyana goyon bayansu ga Gwamna a matsayin wanda zai yi wa APC takarar gwamna.

Sai dai a wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu a madadin kungiyar Pantamiyya Movement, Pantami ya bayyana cewa wannan mataki ya sabawa tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.

Ya kara da cewa bai dace a tilasta wa jam’iyya dan takara ba tare da bin ka’idojin dimokuradiyya da dokokin zabe ba, yana mai kira ga shugabannin jam’iyyar da su mutunta tsarin da doka ta shimfida domin tabbatar da adalci da gaskiya a harkokin siyasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Jami’an Gwamnati Daga Bangarori Daban-Daban Na Kawo Ziyarar Ta’aziyya Gwamnatin Kano

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi Biyo bayan rasuwar ‘yan wasan Kano 22 da…

KHETFUND: Asusun Tallafawa Lafiya Na Jihar Kano Ya Gudanar Da Wasu Ayyuka A Hukumar Samar Da Magunguna Ta Jiha

By: Mukhtar Yahaya Shehu  Asusun tallafawa harkokin lafiya na Jahar Kano , ya…

Hajj 2027: Hukumar Jin Dadin Alhazan Kano Ta Gargadi Ga Maniyyata Kan Mika Passport Kan Lokaci – DG

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Hukumar Jin Dadin Alhazan jihar Kano tana kara gargadin…

Gwamnatin Tarayya Ta Ƙara Sabon Sharaɗi Na Buɗe Asusun Banki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da wani sabon mataki da zai shafi dukkan…