Daga: Ibrahim Sani Gama

Shugaban kwamitin Dattawa na karamar hukumar Ungogo ya nemi masu rike da mukaman siyasa na karamar hukumar Ungogo da su rinka taimakawa masu karamin karfi dake yankunansu domin inganta rayuwar al’ummar jihar Kano.

Alh. Sammani Muhammad Abdulmuminu ne ya ba da wannan shawarar a yayin da yake zantawa da manema labarai a ofishinsa dake kasuwar Singa.   Inda ya ce, wannan lokaci na azumin watan Ramadana, lokaci ne da Allah yake bukatar al’umma su rika taimakekeniya ta ciyarwa ko da kwayar dabino ne.

Shugaban kwamatin ya kuma bukaci Shugabannin da su kara jajircewa wajen samar da ayyukan ci gaba da ka iya taba rayuwar al’ummarsu ta fannoni daban daban, musamman ta hanyar bunkasa kasuwanci da samarwa matasa ayyukan dogaro da kai. Yace, kofarsa a bude take ga wadanda suke bukatar gudunmawa da shawarwari domin bunkasa rayuwar al’umma da farfado da tattalin arzikin kasa da kasuwanci da tsaro da dai sauransu.

Shugaban Kwamatin yabawa Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Alh. Abba Kabir Yusuf bisa aikace-aikacen ci gaba domin bunkasar jihar da al’umma baki daya.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Taura Na Shirin Fuskantar Manyan Sauye-Sauyen Tattalin Arziki – Hambali

Daga: Kabir Getso  Shugaban Karamar Hukumar Taura, Hon. Dr. Shua’ibu Ibn Hambali, ya…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Kaddamar Da Gangamin Allurar Riga Kafin Cutar Shan Inna A Bunkure

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Gwamnatin jihar kano ta jaddada kudirin ta na…

YABO DA KIRA: Shugaban APC na Giginyu Ya Jinjinawa Gwamna Abba, Ya Nemi A Gyara Gadar Badawa

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban ƙungiyar Giginyu Peace kuma Shugaban jam’iyyar APC na…

Matasan Rimin Gado Sun Zargi Barau Da Siyen Kuri’a, Sun Bukaci Gaskiyar Tallafi

Daga: Ibrahim Sani Gama Shugaban kungiyar matasan ‘yan siyasa a karamar hukumar Rimin…