Daga: Kabir Getso 

Shugaban Karamar Hukumar Taura, Hon. Dr. Shua’ibu Ibn Hambali, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba al’ummar yankin za su shaida gagarumin ci gaba, musamman ta fuskar ayyukan raya kasa da tallafin da ake bai wa masu zalla wajen inganta cigaban al’umma.

Yayin ganawarsa da manema labarai, Dr. Hambali ya ce kusancin da shugabannin kananan hukumomi ke da shi da al’umma yana ba su damar fahimtar matsalolin jama’a kai tsaye, lamarin da ya sa ayyukan da suke aiwatarwa ke samun karɓuwa da goyon baya daga kungiyoyin cigaba da shugabannin al’umma.

A cikin dan lokaci, shugaban ya kaddamar da muhimman ayyuka a Taura da kewaye, wadanda suka haɗa da gyaran tituna, inganta hanyoyin sadarwa da kuma tallafa wa makarantun boko da islamiya. Daya daga cikin manyan ayyukan da ya kammala kwanan nan shi ne cika alkawarin sayen filin da ya kai kimanin naira miliyan 2.5 ga makarantar Bakin Dogo Islamic School, domin kara habaka ilimi a yankin.

Dr. Hambali ya bayyana cewa gwamnatin karamar hukumar na aiwatar da wadannan shirye-shirye ne a matsayin daukar darasi daga Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, wanda ya dage wajen ganin an samu cigaba a jiha, musamman a fannonin hanyoyi da ruwa.

A cewar sa, gwamnatin jihar ta ware N292 miliyan domin gina sabbin na’urorin samar da ruwa ta hasken rana a yankuna 19, tare da N81 biliyan na inganta tituna masu tsawon makudan kilomitoci don kara ɗaga darajar tattalin arzikin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Gashash Ya Gargadi ‘Yan Siyasa Kan Furucin “Ko A Mutu Ko Ayi Rai”

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa  Ɗan takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar…

Gwamnatin Tarayya da Kungiyar ASUU Sun Sanya hannu Kan Sabuwar yarjejeniya don ƙarfafa ilimin Manyan Makarantu a Fadin Kasar nan

Gwamnatin Tarayyar da Kungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) sun sanya hannu…

Gawuna Ya Yi Ta’aziyyar Rasuwar Uwa Da ‘Ya ‘Yan Ta 6 Da Aka Kashe

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna…

Zan Yi Amfani Da Shirin GEEP Don Inganta Rayuwar Matasan Nigeria – Hamza Ibrahim Baba

Hamza Ibrahim Baba ya kasance Shugaban hukumar kula da shirin gwamnatin tarayya…