Daga: Mukhtar Yahaya Shehu
Tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano Dr Nasiru Yusuf Gawuna ya bi sahun Al’uma bisa ziyarar Ta’aziyya Unguwar Dorayi Chiranci ga mutumin da aka kashe wa matar sa da ‘ya ‘yan sa 6.
Dr. Nasiru Yusuf Gawuna ya yin ziyarar ta’aziyyar ga wannan mutumin wato Malam Haruna ya bayyana takaici tare da jimamin wannan lamari.

Tsohon mataimakin gwamnan Wanda kuma shi ne shugaban karamar Gudanarwar Bankin bayar da lamunin gidaje na kasa ya yi addu’ar Allah Ya karbi Shahadar su tare da bai wa Malam Haruna hakurin wannan babban rashi.
Cikin sanarwa mai dauke da sa hannun mai taimaka masa ta fannin yada Labarai Abubakar Musa DK Dr. Gawuna ya kuma yi addu’ar Allah ya kare afkuwar hakan a nan gaba. Ya kuma cigaba da bai wa jihar Kano da ma kasa baki daya zaman lafiya.
