Daga: Abdullahi Bashir

Babban Ministan Kudi na ƙasa, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta tsoma baki wajen kayyade farashin fetur ba duk da tashin hankali da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ke janyo sauyin farashin mai a kasuwannin duniya.

Edun ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Gidan Telebijin din Channels a daren jiya Laraba.

Ya ce maimakon gwamnatin ta kayyade farashin fetur, tana shirin bullo da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen rage tasirin yakin kan siyasar duniya na tattalin arzikin Najeriya da rayuwar al’umma.

Ministan ya ƙara da cewa, tuni Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da samar da ƙarin kayan sauya motoci zuwa amfani da iskar Gas guda 100,000 domin bai wa masu motoci damar komawa amfani da iskar Gas din.

A cewarsa, amfani da CNG yana da araha sosai, domin farashinsa yana tsakanin kashi 25 zuwa 30 cikin 100 na farashin fetur, abin da ake sa ran zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da kuma sauƙaƙa wa jama’a nauyin hauhawar farashin mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Gwarzo, Ya Samu Lambar Yabo a Taron Ƙasa da Ƙasa na Masana Jikin Dan Adam

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo,…

Gwamnatin Tarayya Ta Daga Kudin Jarabawar WAEC Da NECO Zuwa N50,000 Daga 2027

Daga: Abdullahi Muhammad Abuja — Gwamnatin Tarayya ta amince da karin kudin jarabawar…

Wata Kungiya Na Neman Zama Jam’iyyar Siyasa a Najeriya

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa A jiya ne kungiyar African Reformation Peace Movement (ARPM)…

Kwamitin Lafiya Na Masarautar Karaye Ya Ziyarci Ma’aikatar Lafiya Ta Jihar Kano

Daga: Mukhtar Yahaya Shehu  Kwamitin lafiya na Masarautar Karaye karkashin jagorancin Matawallen…