Daga: Abdullahi Bashir

Babban Ministan Kudi na ƙasa, Wale Edun, ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta tsoma baki wajen kayyade farashin fetur ba duk da tashin hankali da ake fama da shi a yankin Gabas ta Tsakiya wanda ke janyo sauyin farashin mai a kasuwannin duniya.

Edun ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Gidan Telebijin din Channels a daren jiya Laraba.

Ya ce maimakon gwamnatin ta kayyade farashin fetur, tana shirin bullo da wasu tsare-tsare da za su taimaka wajen rage tasirin yakin kan siyasar duniya na tattalin arzikin Najeriya da rayuwar al’umma.

Ministan ya ƙara da cewa, tuni Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanar da samar da ƙarin kayan sauya motoci zuwa amfani da iskar Gas guda 100,000 domin bai wa masu motoci damar komawa amfani da iskar Gas din.

A cewarsa, amfani da CNG yana da araha sosai, domin farashinsa yana tsakanin kashi 25 zuwa 30 cikin 100 na farashin fetur, abin da ake sa ran zai taimaka wajen rage kuɗin sufuri da kuma sauƙaƙa wa jama’a nauyin hauhawar farashin mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You May Also Like

Rundunar Yaki da Satar Waya a Kano Ta Kama Matashi Kan Zargin Satar Wayoyi da Sayar da Kayayyakin Mata

Daga: Sani Idris Maiwaya Rundunar tsaro ta Anti-Phone Snatching Force (KOSSAP) a…

Abinda Ya Sa Gwamnatin Tarayya Za Ta Fara Aiwatar Da Karin Kashi 40% Na Alawus Ga ASUU

Daga: Abdullahi Bashir Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da muhimman tanade-tanaden jin dadin…

Cigaba Da Ayyukan Alheri Bayan Ramadan Alama Ce Ta Karɓuwar Ibadar Bawa — Sheikh Kamalu Inuwa

Daga: Abdulmajid Habib Tukuntawa Cigaba da aikata kyawawan ayyuka bayan watan Ramadan na…

Gwamnatin Jihar Kano Ta Taya Masarautar Fune Dake Jihar Yobe Murnar Cika Shekaru 25 Akan Karagar Mulki

Daga: Shehu Suleiman Sharfadi  Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo,…