Daga: Ibrahim Sani Gama
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci shugabannin kafafen yaɗa labarai da su riƙa mayar da hankali wajen bincike kan ayyukan gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi kamar yadda suke yi wa gwamnatinsa.
Tinubu ya bayyana hakan ne a daren Juma’a yayin da ya karɓi bakuncin masu mallakar kafafen yaɗa labarai da manyan shugabanninsu a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Aso Rock Presidential Villa.

Ya ce gwamnatinsa ta buɗe tsarin tarayya ta yadda ƙananan hukumomi yanzu ke samun kuɗaɗensu kai tsaye, yana mai cewa ya kamata kafafen yaɗa labarai su sa ido kan yadda ake amfani da waɗannan kuɗaɗe.
“Kada ku riƙa matsa min ni kaɗai. Ku duba abin da ƙananan hukumomi da kuma gwamnatocin jihohi ke yi da kuɗaɗen da suke samu,” in ji shi.
Shugaban ya ƙara da cewa rawar da kafafen yaɗa labarai ke takawa wajen tabbatar da gaskiya da rikon amana a gwamnati tana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasar dimokuraɗiyya.